in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da Theresa May a Beijing
2018-02-01 10:18:06 cri

A yammacin jiya Talata ne a nan birnin Beijing, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da takwaransa ta Birtaniya Theresa May wadda ke ziyarar aiki a kasar Sin, inda suka amince da ci gaba da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen su, haka kuma sun daddale wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama.

Wannan ne karo na farko da Theresa May ta kawo ziyarar aiki kasar Sin tun bayan da ta hau kan kujerar firayin ministar Birtaniya, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya shirya wani biki a babban dakin taron jama'ar birnin Beijing domin nuna mata maraba da zuwa kasar ta Sin. Yayin bikin, 'yan kungiyar badujalan soja ta kasar Sin sun busa taken kasashen Sin da kuma Birtaniya, daga baya Li Keqiang da Theresa May suka kalli faretin girmamawa da sojojin sama da ruwa da kuma kasa na rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin suka shirya.

A halin da ake ciki yanzu, Birtaniya tana shirin ficewa daga kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU, a daidai wannan lokaci, firayin ministar kasar Theresa May ta yi tunani game da kara habaka tattalin arzikin kasar a fadin duniya, wato tana fatan samun ci gaba tare da sauran kasashen duniya, amma ba a yankin Turai kawai ba, kuma kasar Sin tana daya daga cikin muhimman abokan ciniki na Birtaniya, a shekarar 2017, adadin cinikin kayayyaki tsakanin Sin da Birtaniya ya kai dalar Amurka biliyan 79, adadin da ya karu da kaso 6.2 bisa dari idan aka kwatanta da shekarar 2016, kana kasashen biyu suna zuba jari ga junansu, a don haka, ziyarar Theresa May za ta kara mai da hankali kan batutuwa da suka shafi ciniki da zuba jari dake tsakanin sassan biyu. Domin cimma wannan buri, a cikin tawagar ta, ban da wasu ministocin kasar, akwai kuma manajojin manyan kamfanonin Birtaniya kimanin 50, lamarin ya nuna cewa, gwamnatin Birtaniya tana ba da muhimmanci matuka kan hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki dake tsakaninta da kasar Sin.

Yayin shawarwarin da suka yi a jiya, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen biyu wato Sin da Birtaniya su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu tare kuma da kara bude kofa ga juna, musamman ma wajen aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya da hadin gwiwa a fannonin samar da wutar lantarki da makamashin nukiliya da harkar kudi da cinikin fasahohin zamani da sauransu, kana kamata ya yi sassan biyu su kara zuba jari ga junansu, tare kuma da kara adadin cinikin kayayyakin da ake samarwa ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani. Li ya kara da cewa, kasar Sin za ta fara shirye-shiryen gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin biranen Shanghai da Landon a fannin kasuwar hada-hadar kudi a lokacin da ya dace, yana mai cewa, "A shekarar da ta gabata, kamfanonin kasar Sin sun zuba jari da dama a Birtaniya, adadin mafi yawa idan aka kwatanta da adadin jarin da suka zuba a sauran kasashen Turai, kuma yana karuwa sannu a hankali, a don haka muna maraba da kamfanonin Birtaniya domin su zuba jari a kasar Sin, wannan zai ba mu damar cimma burin bude kofa ga juna. Ban da haka kuma, mun tattauna kan hadin gwiwar dake tsakaninmu a fannin harkar kudi, misali Birtaniya za ta ci gaba da fitar takardun lamuni na kudin Sin RMB wato panda, mu ma mun tattauna kan kasuwar hada-hadar kudi tsakanin biranen Shanghai da Landon, duk wadannan sun nuna cewa, sassan biyu wato Sin da Birtaniya suna kokarin daukar hakikanan matakai domin kara bude kofa ga junansu."

Li ya yi nuni da cewa, yanzu tattalin arizkin duniya yana farfadowa, a don haka ya dace a yi amfani da wannan dama mai faraga, domin samun bunkasuwa tare.

A nata bangare, Theresa May ta bayyana cewa, Birtaniya tana sa ran cewa, bayan wannan ziyarar, Sin da Birtaniya za su ciyar da hadin gwiwar dake tsakaninsu gaba yadda ya kamata, kana Birtaniya tana son kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin yayin da ake aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, tana mai cewa, "Muna maraba da damammakin da shawarar ziri daya da hanya daya take samarwa daukacin kasashen duniya, ko shakka babu shawarar za ta kawo wadata da dauwamammen ci gaba ga kasashen Asiya, da ma kasashen duniya baki daya, a matsayinta na kasar dake cikin kasashen da suka kafa bankin zuba jari kan muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a na Asiya wato AIIB, Birtaniya ta shiga shawarar da ake aiwatarwa kai tsaye, muna fatan za a kara kyautata hadin gwiwa bisa shawarar daga duk kan fannoni."

Bayan shawarwarin, firayin ministocin kasashen biyu sun kuma kalli yadda aka daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama tsakanin sassan biyu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China