in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun kasar Algerian sun hallaka mayakan 'yan ta'adda 13
2018-02-01 10:02:54 cri
Dakarun dake yaki da 'yan ta'adda na kasar Algeriya sun kashe mayakan 'yan ta'adda masu dauke da makamai kimanin 13 tun daga farkon watan Janairu, in ji ma'aikatar tsaron kasar.

Majiyar ta kara da cewa, a cikin wannan zangon, biyar daga cikin 'yan ta'addan sun mika kansu tare da gabatar da makamansu ga hukumomin sojin kasar, kana an damke wasu daidaikun mutane 23 wadanda ake zarginsu da tallafawa kungiyoyin 'yan ta'adda.

Sanarwar ta ce, an kashe mayakan 'yan ta'addan 9 a ranar Juma'a a lokacin da dakarun sojin suka kaddamar da samame a mafi yawan yankunan gabashin kasar dake lardin Khenchela, a kusa da kan iyakar kasar da Tunisiya.

A cewar ma'aikatar tsaron kasar, daga cikin 'yan ta'addan da aka hallaka har da wani babban jami'in kungiyar al-Qaeda, wanda aka hallaka shi a ranar Talata a wani surkukin daji dake lardin Jijel, mai nisan kilomita 350 daga gabashin Algiers, babban birnin kasar.

Yana daga cikin jerin sunayen 'yan ta'addan da ake nemansu ruwa a jallo, ana yi masa lakabi da Abu Rawaha al-Qassantini, kuma ya shiga kungiyar 'yan ta'addan ne a shekarar 1994.

Dakarun sojin sun kaddamar da hare hare masu yawa a watan Janairu, kuma sun yi nasarar kwato bindigogi kirar AK47 guda 21, da manyan bindigogi masu sarrafa kansu guda biyu, da boma bomai 47, da kuma harsasai nau'ika iri daban daban.

Majiyar ta kara da cewa, har yanzu dakarun sojin na cigaba da fatattakar 'yan ta'addan a tsaunin dake lardin Medea, mai tazarar kilomita 160 dake kudu maso yammacin Algiers, inda a can ne aka hallaka wasu 'yan ta'adda biyu mafiya hadari. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China