in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon jami'in AU ya bayyana FOCAC a matsayin muhimmin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika
2018-01-31 10:30:56 cri

Erastus Mwencha, tsohon mataimakin shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afrika AU, ya bayyana dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC a matsayin wani muhimmin dandalin karfafa hadin gwiwa tsakanin sassan biyu.

Mwencha, ya kuma yaba da muhimmin tallafin da kasar Sin ke baiwa kasashen Afrika a fannonin ci gaban rayuwa masu yawa.

Da yake zantawa da 'yan jaridu a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Mwencha, ya ce dandalin FOCAC ya kasance a matsayin wani muhimmin ginshiki tun daga lokacin da aka kafa shi, musamman bisa yadda yake kara karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a fannonin da suka shafi zuba jari, kasuwanci, aikin noma, harkokin ma'adanai da dai sauransu.

Ya kara da cewa, ana sa ran taron kolin FOCAC dake tafe wanda za'a gudanar a birnin Beijing, ana fatar zai kunshi wasu muhimman batutuwa da dama, ciki kuwa har da batun nan na shawarar ziri daya da hanya daya da kuma sauran batutuwan ci gaba.

Mwencha ya ce, taron na FOCAC mai zuwa yana da matukar muhimmanci kasancewar Afrika ta gabatar da shirin ajandar ci gaban nahiyar nan da shekarar 2063, kana shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da wasu muhimman batutuwan ci gaba 10 na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China