in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bostswana ta sanya hannu kan yarjeniyoyin yankin ciniki cikin 'yanci na bangarori uku
2018-01-31 10:02:56 cri
A jiya Talata ne, kasar Bostwana ta sanya hannu kan yarjeniyoyin yankin ciniki cikin 'yanci na bangarori uku, matakin da ya kasance zakaran gwajin dafi a ajandar kungiyar tarayyar Afirka game da harkokin cinikayya.

A jawabinsa na sanya hannu kan yarjejeniyar, ministan harkokin zuba jari,cinikayya da masana'antu na Bostsana Vincent Seretse, ya ce yarjeniyoyin yankin ciniki cikin 'yanci(TFTA), za su bunkasa harkokin cinikayya tsakanin kasashen nahiyar,sakamakon yadda aka soke da kuma rage wasu kudaden haraji da ake biya kan wasu kayayyaki da ma wadanda ba a biya musu haraji da kuma yadda aka fadada kasuwar.

Bugu da kari,ana saran yarjeniyoyin za su kasance wata kafa ta bunkasa kungiyin tattalin arzikin nahiyar, matakain da zai kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen dake nahiyar.

A nasa jawabin mataimakin sakataren kungiyar SADC Thembinkosi Mhlongo, ya ce yarjeniyoyin za su bunkasa harkokin cinikayya a nahiyar da kara samar da ci gaba ta hanyar samar da babbar kasuwar bai daya wadda mutane kimanin miliyan 700 za su rika hada-hada a cikin ta, wadda kuma ake fatan za ta samar da GDPn da ya haura dala tiriliyan 1.4.

Ita dai wannan takarda ana kiranta da sunan yarjejeniyar yankin ciniki cikin 'yanci ta kasuwar bai daya ta kasashen dake gabashi da kudancin Afirka(COMESA) da kungiyar kasashen gabashin Afirka(EAC) da kuma kungiyar raya kasashen dake kudancin Afirka (SADC). (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China