A jiya ne dai, hukumar ta dakatar da aiki a makarantun da ta kafa a yankin Gaza, baya ga wasu wuraren jinya da su ma suka dakatar da aiki, in ban da hidima ga wadanda ke cikin mawuyacin hali. Ban da wannan kuma, daruruwan ma'aikatan hukumar sun bazu a kan tituna don gudanar da zanga-zanga.
Kafin wannan mataki, majalisar gudanarwar kasar Amurka ta sanar a ranar 16 ga wata cewa, za ta rage kudaden tallafin da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 65, wanda da ma ake da niyyar baiwa 'yan gudun hijira Falasdinawa ta hannun hukumar UNRWA. Ban da haka, majalisar ta kuma soke wani kudin tallafin na dalar Amurka miliyan 45 da aka yi shirin baiwa Falasdinu a shekarar 2018 da muke ciki.
Yadda kasar Amurka ta ke kokarin dakatar da tallafi ya shafi ayyukan hukumar agaji ta UNRWA matuka, saboda ba ta da kudin da take bukata na gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.(Bello Wang)