in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abdel Fattah Al-Sisi yana kan gaba cikin babban zaben shugaban kasar Masar
2018-01-30 13:21:38 cri
Jiya Litinin, hukumar zaben kasar Masar ta sanar da cewa, an kammala rajistar 'yan takarar babban zaben shugabancin kasa na shekarar 2018, baya ga shugaban kasar mai ci Abdel Fattah Al-Sisi, akwai kuma dan takara guda daya kawai, wato shugaban jam'iyyar Ghad ta kasar Masar Moussa Moustapha Moussa wanda shi ma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a babban zaben.

Kuma bisa hasashen da aka yi, shugaba Abdel Fattah Al-Sisi ne ake ganin zai iya lashe babban zaben da za a yi.

Tun a baya dai hukumar zaben kasar ta sanar da cewa, za a yi zaben shugaban kasar ta ranar 26 zuwa 28 ga watan Maris, idan babu wanda ya samu sama da rabin kuri'un da za a jefa a zagaye na farko na zaben, za a shirya zagaye na biyu na zaben.

Sa'an nan kuma, za a bayyana sakamakon zaben a ranar 1 ga watan Mayu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China