in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU za ta shirya tarukan karawa juna sani game da rikicin dake faruwa a yankin Sahel da tafkin Chadi
2018-01-30 08:46:04 cri

Kungiyar tarayyar Afirka (AU) a takaice za ta shirya tarukan karawa juna sani guda biyu a wani lokaci cikin wannan shekara don tattauna rikice-rikicen dake faruwa a yankin Sahel da tafkin Chadi.

Da yake karin haske game da hakan, kwamishinan kungiyar mai kula da zaman lafiya da tsaro (AUPSC) Smail Chergui, ya ce a cikin 'yan makonni masu zuwa ne za a gudanar da taro game da rikicin yankin Sahel a Nouakchott na kasar Mauritania, yayin da taro na gaba game da rikcin yankin tafkin Chadi zai biyo baya ba da jimawa ba.

Jami'in ya ce, sun tattauna yayin taron kolin kungiyar AU da aka kammala a jiya cewa, akwai bukatar aiwatar da matakan da aka tsara da musayar muhimman bayanai yadda ya kamata tsakanin hukumomin tsaron kasashe mambobin kungiyar.

Chergui ya ce, zai kuma gana da mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin siyasa Jeffrey D. Feltman a gobe Talata, don tattauna yanayin da ake ciki a yankunan biyu da kuma shirye-shiryen gudanar da tarukan biyu dake tafe.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China