in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU ta gabatar da wasu matakai don kara dunkulewar kasashen Afirka a waje guda
2018-01-29 11:04:02 cri

Ana gudanar da taron koli na kungiyar tarayyar Afirka (AU) karo na 30, a hedkwatar kungiyar dake Adis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha da aka bude a ranar 22 har zuwa yau Litinin 29 ga wata. Inda manyan kusoshin kasashen Afirka suka yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da su goyi bayan matakan kafa yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar Afirka, da kafa kasuwar zirga-zirgar jiragen sama ta bai daya ta nahiyar, da tabbatar da saukaka zirga-zirgar 'yan Afirka tsakanin ko wane bangaren nahiyar tare da jigilar kayayyaki cikin 'yanci, ta yadda za a samu damar kara dunkulewar kasashen nahiyar waje guda.

A watan Yunin shekarar 2015 ne, mambobin kungiyar AU suka kaddamar da shawarwari dangane da kafa babban yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar Afirka. Daga bisani ake kokarin cimma matsaya, musamman ma ta fuskokin huldar dake tsakanin kungiyoyin hadin gwiwar yankuna daban daban na nahiyar da yankin ciniki cikin 'yancin da ake neman kafawa, da dangantakar dake tsakanin kasashen nahiyar daban daban.

Manufar kafa yankin ciniki cikin 'yanci a nahiyar Afirka, ita ce rage kudin harajin kwastam da ake karba, da kau da shingayen da suke gurgunta harkokin cinikayya, da saukaka musayar kayayyaki, aikin hidima, da hada-hadar ciniki cikin 'yanci tsakanin wurare daban daban na nahiyar Afirka, a karshe za a samu damar dunkulewar sassa daban daban na nahiyar, ta yadda za su zama wata babbar kasuwa ta bai daya.

Sa'an nan a bangaren harkar zirga-zirgar jiragen sama, kasashen Afirka sun nuna aniyyar kafa kasuwar bai daya, don kau da shingayen da ke kawo tsaiko tsakanin kasashe daban daban dake nahiyar Afirka a wannan fanni. Ta wannan mataki, jiragen sama za su samu damar yin zirga-zirga tsakanin kasashen dake nahiyar cikin 'yanci, haka kuma za a rage kudin da ake bukata a fannin sufuri ta jiragen sama.

Tun a shekarar 2015 kungiyar AU ta tsai da niyyar kafa kasuwar zirga-zirgar jiragen sama ta bai daya a nahiyar, kamar yadda yake kunshe cikin ajandar raya nahiyar Afirka nan da shekarar 2063.

A nasa bangare, babban kwamishinan kungiyar AU mai kula da samar da kayayyakin more rayuwar jama'a da harkar makamashi, Amani Abou-Zeid, ya yi bayani kan fa'idar da aikin kafa kasuwar bai daya za ta samar wa tattalin arzikin kasashen Afirka, inda ya ce, bayan da aka kaddamar da aikin kafa kasuwar a ranar 28 ga wata, ana sa ran ganin samun karin guraben aikin yi kai tsaye da yawansu ya kai dubu 300, gami da karin wasu guraben aikin yi fiye da miliyan 1 a wani fannin.

A cewar jami'in, wasu kasashe 23 daga cikin kasashe mambobin kungiyar AU 55 sun riga sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa kasuwar bai daya a fannin zirga-zirgar jiragen sama. Jami'in ya yi kira ga sauran kasashen dake nahiyar Afirka da su ma su shiga a dama da su.

Yanzu wasu matsalolin da suke hana ruwa gudu ga yunkurin kafa kasuwar bai daya ta zirga-zirgar jiragen sama sun hada da ra'ayin rufe kofa da wasu kasashe suka nuna kan harkar sufurin jiragen sama, da mawuyacin halin da wasu kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama ke fuskanta, gami da yadda ake kayyade damar samun izinin shiga wata kasa.

Game da bukatar 'yancin zirga-zirga tsakanin kasashen nahiyar, tun daga shekarar 2014, mambobin kungiyar AU sun cimma matsayar samar da takardar fasfot nahiyar Afirka ta bai daya, da zummar saukaka zirga-zirgar jama'a, da kayayyaki tsakanin kasashen nahiyar daban daban, da ciyar da tattalin arzikin daukacin nahiyar gaba.

A ganin Madam Cessouma Minata Samate, babbar kwamishinar kungiyar AU mai kula da harkar siyasa, yadda ake samun damar shiga ko wane bangaren nahiyar cikin sauki, da jigilar kayayyaki cikin 'yanci, shi ne matakin farko na kokarin dunkulewar kasashen nahiyar waje guda.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China