in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka 6 sun samu lambobin yabo kan yaki da cutar malaria
2018-01-29 09:38:58 cri

A jiya Lahadi ne wasu kasashen Afirka guda 6 suka lashe lambobin yabo saboda nasarorin da suka samu a yaki da cutar zazzabin cizon sauro na malaria, a dai dai gabar da nahiyar ke fafutuwar ganin bayan wannan cuta nan da shekarar 2030.

An karrara wadannan kasashen ne da lambobin yabon shugabannin kasashen Afirka(ALMA) a yayin taron kolin kungiyar AU karo na 30 dake gudana a hedkwatar kungiyar a birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Ka'idojin da aka bi wajen bayar da lambobin yabo na wannan shekarar su ne tasirin da rage cutar ya haifar da kuma irin ci gaban da aka samu dangane da dabarun hukumar lafiya ta duniya na kawar da cutar nan da shekarar 2020(GTS).

An baiwa kasashen Madagascar da Senegal da Gambia da Zimbabwe lambobin yabo kan nasarorin da suka cimma wajen rage yaduwar cutar da kaso 20 cikin 100 tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016. Yayin da kasashen Aljeriya da Comoros suka samu lambobin yabo, na kasashen dake kan turbar cimma nasarar dabarun yaki da cutar nan da shekarar 2020 da kuma yadda suka yi nasarar rage yaduwar cutar da a kalla kaso 40 cikin 100.

Shugabannin nahiyar Afirka sun himmatu wajen ganin bayan cutar nan da shekarar 2030, kamar yadda yake kunshe cikin ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China