Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi kira ga kasashen nahiyar Afirka da su tashi tsaye wajen yakar matsalar cin hanci dake zama Alla-kakai ga ci gaban nahiyar.
Shugaban ya yi wannan kiran ne jiya Lahadi yayin da yake jawabi a taron kolin kungiya tarayyar Afirka dake gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha. Ya kuma jaddada tasirin da matsalar cin hanci da satar kudade suke haifarwa ga harkokin jin dadin jama'a da tattalin arziki. A don haka ya bukaci kasashe mambobin kungiyar, da su yi kokarin samar da tsarin shugabanci da hukumomi na gari wajen ganin an kawar da matsalar cin hanci da ma abubuwan dake hana ci gaban nahiyar.
Kungiyar AU dai ta zabi shugaba Buhari a matsayin jagoran yaki da cin hanci da rashawa. Matsalar da Buharin ya ce ta lalata duk wani tsari na shugabanci.(Ibrahim)