Da yake jawabi a lokacin taron kolin kungiyar tarayyar Afrika karo na 30 a Addis Ababa, babban birin kasar Habasha, Emmanuel Nnadozie, babban sakataren gidauniyar bunkasa cigaban kasashen Afrika (ACBF), yace adadin kudaden da nahiyar ke tafka hasararsu a sakamakon ayyukan rashawa yana matukar gurgunta cigaban nahiyar.
A halin yanzu, binciken da gidauniyar ACBF ta gudanar ta gano Afrika na yin hasarar akalla dala biliyan 50 a duk shekara a sanadiyyar ayyukan da suka shafi rashawa, sai dai Nnadozie ya lura cewa, mafi yawan kudaden dake salwanta daga Afrika a sanadiyyar ayyukan rashawar ana adana su ne a kasashen da bana Afrikan ba, lamarin da ke haifar da koma baya ga nahiyar.
Nnadozie yace matsalar rashawa al'amari ne da ya shafi dukkan duniya baki daya, ba wai matsala ce data shafi iya Afrika ba, ko ina ka zagaya a duniya akwai matsalar rashawa, don haka batun magance rashawa a Afrika, al'amari ne dake bukatar goyon bayan kasa da kasa.