in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar kasuwancin Sin ta yi watsi da ra'ayin hana ta damar kasancewa a WTO
2018-01-26 11:46:51 cri

Kwanakin baya ofishin wakilan cinikin kasar Amurka ya fitar da wani rahoto cewa, shigar da kasar Sin cikin kungiyar ciniki ta duniya wato WTO kuskure ne da aka aikata, har an bayyana cewa, kila za a gudanar da bincike kan kasar Sin game da karya ikon mallakar fasaha da ta yi. Game da hakan, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana jiya cewa, rahoton ba shi da dalili ko kadan, kuma bayyane take cewa an fitar da shi ne domin ba da kariya ga cinikin kasar Amurka, kuma gwamnatin kasar Sin ta nuna rashin amincewa da rahoton.

Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya jaddada cewa, gudanar da hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka zabi ne daya kacal da ya fi dacewa da moriyar sassan biyu, kasar Sin za ta dauki matakai domin yaki da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya domin kare hakkinta bisa ka'ida, yana mai cewa, "Mun duba wannan rahoto sosai, mun lura cewa, ba shi da dalili ko kadan, kuma ya saba da ra'ayoyin da Amurka ta nuna a baya. A bayyane take cewa an fitar da rahoton ne domin ba da kariya ga cinikayya, a don haka kasar Sin ta nuna kin amincewa da shi. Muna ganin cewa, kamata ya yi a raya tattalin arzikin kasuwa bisa tsarin tattalin arzikin da ya dace da yanayin da kasar ke ciki, amma bai kamata ba a tsara hakan bisa ma'aunin wata kasa ita kadai kamar yadda take so ba."

Gao Feng ya kara da cewa, bayan da kasar Sin ta shiga WTO, ta samar da damammakin ci gaba, har ta sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Bisa alkaluman da MDD da IMF da sauran kungiyoyin kasa da kasa suka samar, an ce, a shekarar 2017 da ta gabata, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa kan ci gaban tattalin arzikin duniya, har ya kai kaso 30 bisa dari, kana tun bayan da aka shigar da kasar Sin cikin WTO, sai matsayin harajin kwastan na kasar Sin ya ragu daga kaso 15.3 bisa dari zuwa kaso 9.8 bisa dari.

Ban da haka kuma, Gao Geng ya yi nuni da cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tana kara bude kasuwarta sannu a hankali, adadin manufofiin da aka fitar domin kayyade shigar da kayayyakin kere-kere daga ketare ya ragu da har sama da 50 idan aka kwatanta da farkon lokacin da aka shigar da kasar cikin WTO. Game da sana'o'in dake shafar aikin samar da hidima da yawansu ya kai 160 kuwa, kasar Sin ta taba yin alkawarin cewa, za ta bude sana'o'i 100, amma yanzu ta bude kusan 120. Abu mafi muhimmanci shi ne Amurka ita ma ta samu moriya daga wajen, Gao Feng ya ce, "A cikin wadannan shekaru 16 da suka gabata, wato tun bayan da kasar Sin ta shiga WTO, adadin kayayyakin da Amurka ta fitar zuwa kasar Sin ya karu da kaso 500 bisa dari, adadin da ya zarta kason karuwarsa ga sauran kasashen duniya da bai wuce kaso 90 bisa dari kacal ba. Yanzu haka kasar Sin ta zama kasa ta uku wadda take shigo da kayayyakin Amurka a fadin duniya, amma a baya matsayin ta bai wuce kaso takwas kacal ba. Ko shakka babu shigar da kasar Sin cikin WTO, baya ga damammakin ci gaba da ya samarwa Amurka, a hannu guda ya kuma samar da damammakin ga sauran mambobin kungiyar."

Tun daga farkon bana, Amurka tana ci gaba da kayyade adadin kayayyakin samar da lantaki ta hasken rana, da manyan injuna na wanke tufafin da ta shigar daga sauran kasashe, kana yayin taron Dawos da ake gudanarwa, ministan kasuwancin Amurka Wilbur Ross ya bayyana cewa, kila ne kasarsa za ta gudanar da bincike kan kasar Sin game da karya ikon mallakar fasaha. Duk wadannan sun nuna cewa, kila a bude yakin ciniki tsakanin Sin da Amurka.

Gao Feng ya bayyana cewa, huldar dake tsakanin sassan biyu ta samu ci gaba sannu a hankali a cikin shekaru arba'in da suka gabata, shi ya sa suke dorago ga juna, musamman ma wajen huldar tattalin arziki da ciniki. Idan sassan biyu suka yi hadin gwiwa, to, za su amfana tare, amma idan sassan biyu suka yi yaki, tabbas za su yi hasara tare. Gao Feng ya ce, "Gudanar da hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka zabi ne daya tak da ya fi dacewa da moriyar sassan biyu, kuma kasar Sin tana nacewa ga matsayin nan na yin hadin gwiwa a ko da yasuhe. Muna fatan rigimar ciniki dake tsakanin sassan biyu za ta saukaka ta hanyar da ta dace, amma idan aka dauki matakin da bai dace da ka'idar WTO ba, to, kasar Sin za ta dauki matakin da ya dace domin kare hakkinta bisa ka'ida."

A shekarar 2017, kasashe da yankuna a fadin duniya da yawansu ya kai 21, sun gudanar da bincike kan kayayyakin kasar Sin har sau 75, adadin kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 11, Gao Feng ya sake jaddada cewa, kasar Sin ba ta yarda da irin wannan matakin da aka dauka ba, saboda bai dace da ka'idar WTO ba, yana fatan za a daidaita rigingimun ciniki ta hanyar yin shawarwari da kuma hadin gwiwa, wanda da haka ne za a kafa tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China