Liu Zhenmin ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin ya bayyana wannan tunanin a dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya da aka gudanar a shekara daya da ta gabata. A cikin wannan shekara, tunanin nasa ya taka muhimmiyar rawa yayin da ake gudanar da ayyuka a fannoni daban daban, kana shugabannin hukumomin kasa da kasa sun yi amfani da wannan tunani yayin da suke tattauna kan tsarin raya duniya na bai daya.
Liu Zhenmin ya jaddada cewa, ana bukatar kasa da kasa da su yi kokari tare, wajen sa kaimi ga raya duniya bisa tsarin bai daya, da hada wannan da aiwatar da ajandar samun bunkasuwa mai dorewa ta shekarar 2030 ta MDD. (Zainab)