in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira ga sa kaimi ga tsarin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama
2018-01-25 12:07:22 cri

An gudanar da taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya karo na 48 a birnin Davos dake kasar Switzerland. A safiyar ranar 24 ga wata, wani jami'in kasar Sin ya yi jawabi a gun taron, inda ya yi bayani game da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da manufofin tattalin arziki da Sin za ta gudanar a shekaru masu zuwa.

A wannan rana, mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne darektan ofishin kula da harkokin kudi da tattalin arziki na gwamnatin kasar Sin Liu He ya yi jawabi mai taken "sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci da samun bunkasuwar tattalin arziki da wadata a duniya yadda ya kamata", wanda ya jawo hankalin wakilai daga bangarorin siyasa da ciniki masu halartar taron. Shugaban gudanarwa na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya Klaus Schwab ya shugabanci taron jawabi a wannan karo na dandalin tattaunawar. Schwab ya bayyana cewa, jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping a gun taron dandalin tattaunawar a shekarar bara yana da babbar ma'ana, ya yi imani da cewa, jama'a suna begen sake sauraron ra'ayoyi daga kasar Sin. Schwab ya ce,

"Makomar kasar Sin tana da nasaba da tattalin arzikin duniya, musamman a karkashin yanayin da ake ciki na fuskantar ra'ayin bada kariya ga tattalin arziki, da barazanar hamayyar ciniki a duniya. Don haka, bayan da shugaba Xi Jinping ya yi jawabi a bara, muna farin ciki sosai da saurara ra'ayin da malam Liu He zai gabatar game da tattalin arzikin Sin na nan gaba."

A cikin jawabinsa, Liu He ya bayyana cewa, jawabin shugaba Xi Jinping a bara a birnin Davos ya samu karbuwa sosai a fadin duniya. A cikin shekara daya da ta gabata, Sin ta aiwatar da kiran da shugaba Xi Jinping ya yi, da sa kaimi ga raya tsarin tattalin arzikin duniya na bai daya. Liu He ya bayyana cewa,  

"A bara, shugaba Xi Jinping ya yi jawabi mai taken 'daukar alhaki tare da sa kaimi ga samun bunkasuwa a duniya tare', inda ya nuna goyon baya ga sa kaimi ga raya tsarin tattalin arzikin duniya na bai daya, wanda ya samu karbuwa sosai a fadin duniya. A cikin shekara daya da ta gabata, Sin ta gudanar da ayyuka bisa kiran shugaba Xi Jinping, da yaki da ra'ayin bada kariya ga tattalin arziki ta hanya iri iri, da tabbatar da ikon mallakar ilmi ko kayyayaki, da sa kaimi ga ciniki, da fadada shigar da kasuwar kasar Sin."

Daga baya, Liu He ya yi bayani game da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, da manufofin tattalin arziki da Sin za ta gudanar a shekaru masu zuwa. Ya ce, taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 ya gabbatar da sabbin shugabannin kwamitin tsakiya na JKS karkashin shugaba Xi wanda shi ne jigo, da mai da tunanin tsarin gurguzu mai alamar kasar Sin na sabon zamani na Xi Jinping a matsayin tunanin gudanar da ayyukan raya kasar Sin, da tabbatar da manufofin tattalin arzikin Sin da za a gudanar a shekaru masu zuwa.

Liu He ya jaddada cewa, taken dandalin tattaunawar a wannan karo shi ne "kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama a duniya dake rarrabe". Babu kuma wata kasa da za ta iya fuskantar matsalolin sauyin yanayi, da bunkasuwar fasahohin zamani, da yaki da ta'addanci da sauransu ita kadai. Don haka, Liu He ya bada shawara cewa,

"Ya kamata mu kara fahimtar juna, da hakuri da juna, da yin imani da juna, da kara yin hadin gwiwa bisa halin da ake ciki, da sa kaimi ga raya tsarin tattalin arzikin duniya na bai daya, mai bude kofa ta adalci da hadin gwiwa, da kuma kafa sabuwar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa cikin girmama juna da adalci, da hadin gwiwa da samun moriyar juna, da kuma kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China