in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban Zimbabuwe ya yi maraba da masu zuba jari na kasa da kasa
2018-01-25 11:05:12 cri
A jiya Laraba, sabon shugaban kasar Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa wanda a halin yanzu ke halartar taron dandalin tattalin arzikin duniya a garin Davos na kasar Switzerland, ya bayyana cewa, Zimbabuwe na maraba da masu zuba jari na kasa da kasa da su zuba mata jari, don taimakawa ga farfado da tattalin arzikin kasar.

Mr. Mnangagwa ya jaddada cewa, kofar Zimbabuwe a bude take, kuma farfado da tattalin arzikin kasar aiki ne da gwamnatin kasar ke sanyawa matukar muhimmanci, kuma kasar za ta sassauta matakan da suka kayyade masu zuba jari na kasashen waje.

Mr. Mnangagwa ya kara da cewa, sabuwar gwamnati za ta gyara dokokin da suka kawo cikas ga masu zuba jari, kuma ta riga ta gyara dokar da ta kayyade yawan hannayen jari da 'yan kasar ke rike da ya kai sama da 51%, abin da kuma zai shafi masana'antun hakar lu'ulu'u da zinarin Platinum ne kawai, a maimakon nau'o'in masana'antu baki daya.

Ban da haka, Mr. Mnangagwa ya kuma ambaci batun siyasar kasar, inda ya ce, "Tsarin mulki ya bukaci a gudanar da zaben shugaban kasa a shekaru biyar biyar, kuma wa'adin shugabanci na yanzu zai cika a watan Yuli, don haka za mu gudanar da zaben kafin watan Yuli."(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China