in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zambia ya bukaci goyon bayan IAEA game da cin moriya daga makamashin nukiliya
2018-01-25 10:02:03 cri

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu, ya yi kira ga hukumar dake lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ko IAEA a takaice, da ta tallafawa kasar sa dake kudancin nahiyar Afirka da dama ta cin gajiyar makamashin nukiya.

Shugaba Lungu ya ce, Zambia na bukatar kayayyakin aiki na zamani, da tsare tsaren gudanar da binciken kimiyya, wadanda za su baiwa masanan kimiyyar kasar damar sada al'umma da moriyar dake tattare da makamashin nukiliya.

Shugaban kasar dai na wannan tsokaci ne yayin ganawar sa da babban daraktan hukumar ta IAEA Yukiya Amano, a fadar gwamnatin kasar ta Zambia. Ya ce, amfani da fasahohin nukiliya na daya daga muhimman matakai da za su habaka ci gaban Zambia.

A nasa bangaren kuwa, shugaban hukumar ta IAEA cewa ya yi, hukumar za ta sada Zambia da dukkanin kwarewa da sanin makamar aiki da ake bukata, wajen tsara dokokin aiki a fannin amfani da kimiyyar makamashin nukiliya, ciki hadda kafa cibiyar sarrafa makamashin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China