in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta jaddada bukatar magance matsalar karancin kwararru don cimma nasarar ci gaban Afrika
2018-01-25 09:44:41 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta jaddada bukatar shawo kan matsalar karancin kwararru domin cimma muradun karni na ci gaban nahiyar Afrika, ta hanyar baiwa mata da 'yan mata karin damammaki wajen ba su ilmi.

Kwamishiniyar AU mai kula da sashen samar da kwararru, da ci gaban kimiyya da fasaha, Sarah Anyang Agbor, ta bayyana a lokacin taron koli na kungiyar AU wanda ke gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha cewa, za'a iya cimma nasarar ajandar ci gaban nahiyar Afrika da samar da kyakkyawar makoma da zaman lafiya da kwancinyar hankali a nahiyar nan da shekarar 2063 ne kadai idan aka samu kwararru 'yan asalin nahiyar ta Afrika, wadanda za su ja ragamar aiwatar da ajandar ci gaban nahiyar.

To sai dai kuma, Agbor ta bayyana a lokacin taron manema labarai game tattaunawa kan al'amurramn mata da 'yan mata cewa, Afrika tana fama da karancin kwararru a fannin ci gaban fasahar sadarwa ICT, da kuma bangaren kimiyya, fasahar, kere kere da lissafi wato STEM, kwararrun da ake da su da wadanda suka kammala manyan makarantun gaba da sakandare a wadannan fannoni sun yi matukar karanci, ta yadda ba za su iya cike gibin bukatar da ake da ita ba.

Haka zalika, ta kuma jaddada bukatar karfafawa mata gwiwa wajen ba su damar karantar fannonin kimiyya, fasaha, kere kere da lissafi, a cewarta, wadannan fannoni maza ne suka kankane su, ta ce dole ne a baiwa mata dama idan ana son cimma burin ci gaban muradun karni na Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China