Yau Talata a nan Beijing, Zhang Dejiang, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya yi shawarwari da Meshal Faham M. Alsulami, shugaban majalisar kungiyar kawancen kasashen Larabawa, inda ya ce, ziyarar aiki da mista Alsulami yake yi a nan kasar Sin ita ce ta farko a tsakanin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisar kungiyar kawancen kasashen Larabawa, wadda take da muhimmiyar ma'ana wajen kyautata huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Larabawa. Kasar Sin na son hada kai da kasashen Larabawa domin ganin dankon zumuncin da ke tsakaninsu ya kara haifar da sakamako mai kyau.
A nasa bangaren, mista Alsulami ya ce, kasashen Larabawa sun yaba muhimmiyar rawa da kasar Sin take takawa wajen wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, kana sun amince tare da goyon bayan shawarwari guda 4 da Sin ta gabatar dangane da warware batun Palesdinu. (Tasallah Yuan)