in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron koli na AU ya mai da hankali kan dakile cin hanci da rashawa
2018-01-23 10:52:32 cri

A jiya Litinin, aka kaddamar da taron koli karo na 30 na kungiyar tarayyar Afirka AU a Addis Ababa, fadar mulki kasar Habasha. Babban taken taron koli na kungiyar tarayyar Afirka AU a wannan karo shi ne "Neman samun nasara a kokarin dakile cin hanci da rashawa: wata hanyar da ake bi don samun sauyawar yanayi da cigaba mai dorewa a nahiyar Afirka". Bisa wannan take, manyan kusoshi mahalarta taron suna mai da hankali kan aikin yaki da cin hanci da rashawa a kasashen Afirka, da yin kwaskwarima ga tsare-tsaren kungiyar AU, gami da dinkewar kasashen dake nahiyar Afirka a waje guda.

Shugaban kungiyar AU Moussa Faki, ya halarci wani taron majalisar zaunannun wakilan kasashen Afirka a taron kolin kungiyar AU, wanda aka kira jiya a gefen taron kolin kungiyar na wannan karo, inda ya furta cewa, dalilin da ya sa aka mai da yakar cin hanci da rashawa babban take na wannan taro, shi ne domin matsalar na kara tsamari, haka kuma ta haifar da illa ga yunkurin kasashen Afirka na raya tattalin arziki, da kyautata yanayin zamantakewar al'umma, da kuma daidaita tsarin siyasa.

Wani jami'in kungiyar AU mai kula da aikin yaki da cin hanci da rashawa ya ce, matsalar cin hanci ta hana ruwa gudu ga niyyar, kuma kasashen Afirka na samun ci gaba mai dorewa cikin lokaci mai tsayi nan gaba, wadda ta riga ta zame ma nahiyar Afirka babban kalubalen da take fuskata. Sauran fannonin da matsalar ta shafa, a cewar jami'in, sun hada da tsaro, da kare hakkin jama'a, da dai sauransu.

Haka zalika, kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta bayyana cikin shafin Internet nata cewa, a cikin shekaru fiye da 20 da suka gabata, nahiyar Afirka ta samu ci gaba cikin sauri a bangarorin tattalin arziki da zaman al'umma, amma duk da haka, matsalar cin hanci da rashawa ta zama wani abun da ya ki ci ya ki cinyewa, lamarin da ya raunana imanin da jama'ar kasashen Afirka suke da shi kan gwamnatocinsu, tare da haddasa rashin daidaito tsakanin al'ummomi. Ganin haka ya sa mutane da yawa suka yanke kaunarsu kan buri na raya kimiyya da fasaha, da habaka cinikayya a Afirka, da kuma dunkulewar tattalin arzikin nahiyar da na sauran sassan duniya.

Sa'an nan game da batun kwaskwarima ga tsare-tsaren kungiyar AU, ta la'akari da muhimmiyar rawar da kungiyar take takawa a kokarin neman cimma burin raya tattalin arzikin nahiyar Afirka bisa "Ajandar shekarar 2063", shugabannin kasashen Afirka sun cimma matsaya kan gudanar da gyare-gyare ga tsarin kungiyar AU, da nufin tabbatar da ganin kungiyar ta dinga samar da hidimomi ga jama'ar nahiyar Afirka, da kare ra'ayin tushe na kungiyar, wato hadin gwiwa, da samun 'yanci, gami da daidaito.

A cewar Moussa Faki, shugaban kungiyar AU, aikin kwaskwarima ga tsare-tsaren kungiyar na da muhimmanci matuka, domin ta hanyar gudanar da aikin za a samu damar kara ingancin aikin kungiyar, da sanya ta zama mai zaman kanta a fannin kudi.

An ce babban matakin da ake neman dauka bisa kwaskwarimar da za a yi a wannan karo, shi ne daidaita tsarin kungiyar AU ta fuskar tara kudi. Kafin haka, a wajen taron kolin kungiyar AU karo na 27 da ya gudana a shekarar 2016, an riga an zartas da kuduri na tara kudi bisa radin kai, inda ake sa ran matakin zai taimakawa kungiyar AU samun isashen kudi daga bangarori daban daban, maimakon dogaro kan tallafin da ake bayarwa.

Bisa wannan kudurin da aka zartas, wanda ya fara aiki daga watan Janairun shekarar 2017, kan wasu kayayyakin da ake shigar da su cikin nahiyar Afirka, ana karbar harajin da yawansa ya kai 0.2%. Kudin da ake baiwa kungiyar AU, domin ta gudanar da harkokinta na fannoni daban daban.

Ban da wannan kuma, wani batun da ake tattaunawa a wajen taron kolin kungiyar AU a wannan karo shi ne, sa kaimi ga dinkewar kasashen nahiyar Afirka waje guda, inda ake neman baiwa 'yan Afirka damar shiga ko wane yanki na nahiyar cikin 'yanci.

An ce yunkurin kafa wani yankin cinikayya mai 'yanci tsakanin kasashen Afirka daban daban, shi ma zai taimakawa kokarin dinkewar tattalin arzikin nahiyar waje guda.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China