in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gabon na bukatar koyon nasarorin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin
2018-01-22 13:09:27 cri

A kwanakin baya ne, babban sakataren jam'iyyar demokuradiyya mai mulki a kasar Gabon, wato jam'iyyar PDG, Mista Eric Dodo Bounguendza, ya zanta da 'yan jaridun kasar Sin, inda ya ce, kasarsa na bukatar koyon yadda jam'iyyar kwaminis mai mulki a kasar Sin take gudanar da ayyukanta, kana, jam'iyyar PDG na matukar fatan karfafa mu'amala da hadin-gwiwa da kasar Sin.

Mista Bounguendza ya bayyana cewa, jam'iyyar PDG ta Gabon, da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suna da dadadden zumunci har na tsawon shekaru sama da talatin, inda jam'iyyun siyasun biyun suka baiwa juna taimako da goyon-baya, har ma hadin-gwiwarsu ya inganta sosai.

A kwanakin baya ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gudanar da ziyarar aiki Gabon, haka kuma shugaban majalisar dattawan Gabon ya ziyarci kasar Sin. Wannan ya shaida cewa, jam'iyyun siyasun kasashen biyu na kara yin mu'amala tsakaninsu.

A watan karshe na shekarar da ta gabata, yayin da yake halartar babban taron manyan jami'ai na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da na jam'iyyun siyasun kasa da kasa a birnin Beijing, Bounguendza ya ce, nan da shekaru biyar masu zuwa, ya kamata jam'iyyun siyasun Sin da Gabon su karfafa hadin-gwiwa a fannin horas da mahukuntansu, inda ya ce, jam'iyyar kwaminis ta Sin ta kafa wasu makarantu na horas da jami'anta daga kananan hukumomi, abun da ya burge shi sosai.

A cewar Bounguendza, jam'iyyar PDG ta Gabon ta yarda da akidun jam'iyyar kwaminis ta Sin wajen tafiyar da harkokinta, inda ya ce, a gun taron jam'iyyar PDG da aka yi kwanan baya, shugaban kasar Ali Bongo ya gabatar da jawabin dake jaddada muhimmancin inganta ka'idoji da manufofi na jam'iyyar PDG.

Bounguendza ya kara da cewa, inganta ka'idoji gami da manufofi na jam'iyya, muhimmiyar akida ce ta jam'iyyar PDG har ma ta duk kasar Gabon baki daya, shi ya sa ya kamata a jaddada muhimmancin sake farfado da ka'idojin jam'iyyar, musamman a fannin yaki da matsalar cin hanci da karbar toshiya. A cewar Bounguendza, hakan na da babbar ma'ana ga daga kwarjinin jam'iyyar PDG, don ta zama abar koyi ga dukkan al'ummar kasar, ta kuma jagorance su wajen samun ci gaban kasa mai dorewa.

Bounguendza ya yi nuni da cewa, a cikin tsawon shekaru sama da talatin, jam'iyyar kwaminis ta Sin ta samar da dimbin tallafi da taimako ga bangaren Gabon, inda baya ga taimakawa ga inganta muhimman ababen more rayuwar jama'a a Gabon, ciki har da gina hanyoyin mota da ababen motsa jiki, Sin ta kuma baiwa Gabon taimako a fannin kyautata zaman rayuwar al'umma, ciki har da ba da tallafin jinya, da gina wasu asibitoci da dama a kasar ta Gabon.

Mista Bounguendza ya gayawa 'yan jaridun kasar Sin cewa, har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da karfafa mu'amala da hadin-gwiwa tsakanin Sin da Gabon. Yana mai fatan irin hadin-gwiwar kasashen biyu zai amfani karin sassan Gabon, da bayar da gudummawa ga raya tattalin arziki daga fannnoni daban-daban a kasar.

A cewar Bounguendza, kasar Sin abar koyi ce a fannin karfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashen dake tasowa a duk fadin duniya baki daya, yayin da kasar Gabon ke fatan samun ci gaba sakamakon taimakon da kasar Sin ke samar mata.

A watan Satumbar shekarar da muke ciki, za'a yi taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka wato taron kolin FOCAC a nan birnin Beijing. Mista Bounguendza ya bayyana cewa, tun da kasar Sin da kasashen Afirka suka fara yin hadin-gwiwa da mu'amala tsakaninsu har zuwa yanzu, suna nacewa ga bin akidar kawowa juna moriya. Yanzu kuma an daga matsayin taron FOCAC zuwa taron kolin dake kunshe da shugabannin kasashen Afirka daban-daban, hakan ya sa kasar Gabon da sauran wasu kasashen Afirka suka kara maida hankali kan batun habaka tattalin arzikin kasa daga dukkanin fannoni. Mista Bounguendza ya nuna cewa, albarkatun kasa na daukar babban kaso na daukacin kayan da ake fitarwa daga kasashen Afirka, haka kuma kasashen Afirka na dogaro kusan kacokan kan albarkatun man fetur, amma ba su maida hankali sosai kan raya sana'ar kere-kere ba, don haka tattalin arzikinsu bai bunkasa da sauri ba. Ya ce, ita kuwa kasar Sin, ta samu dimbin nasarori a fannin habaka tattalin arziki daga fannoni daban-daban, matakin da ya kamata kasashen Afirka su yi koyi da shi. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China