Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Chen Zhu, ya halarci taron a matsayin shugaban tawagar wakilan kasar Sin.
A yayin taron, Mr Chen, ya gabatar da jawabi inda ya bayyana cewa, a yayin cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 19, kasar Sin ta bude wani sabon shafi na neman bunkasuwa. Kuma, tana son yin hadin gwiwa da kasashen dake yankin Asiya da Pacifik wajen kafa dangantakar abokantaka iri na nuna fahimtar juna da kuma neman ci gaba tare, ta yadda za a cimma moriyar juna, yayin gina wata makoma mai haske ga al'ummomin kasa da kasa.
Bugu da kari, a yayin taron, Chen Zhu, ya halarci taron ganawar babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta kasar Vietnam Nguyen Phu Trong.
Sa'an nan, ya kuma gana da shugaban majalisar dokokin kasar Vietnam Nguyen Thi kim Ngan, da shugaban majalisar Hural na kasar Mongoliya Zandankhuu Enkhbold. (Maryam)