in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zartas da shawarar gyara tsarin mulki a wani taron jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin
2018-01-19 19:36:28 cri

Tsakanin ranekun 18 zuwa 19 ga wannan wata, an gudanar da taro karo na 2 na daukacin mambobin kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, jam'iyyar dake kan ragamar mulkin kasar, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Inda mahalarta taron sun zartas da shawarar gyara wasu bayanai a cikin tsarin mulkin kasar.

Mahalarta taron sun jaddada cewa, an riga an shiga cikin wani sabon zamani wajen raya tsarin gurguzu mai halayyar musamman na kasar Sin, saboda haka ana bukatar daidaita tsarin mulkin kasar, don ya kunshi wasu sabbin ra'ayoyi da tsare-tsaren gudanar da mulki.

An kara da cewa, matakin da aka dauka na neman sanya wasu sabbin manufofin da aka tabbatar da su a wajen taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na 19 musamman ma "Tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki", cikin tsarin mulkin kasar, ya nuna yadda ake kokarin daidaita tsare-tsaren tushe na kasar don neman cimma burin kara raya kasar a nan gaba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China