Lu Kang ya bayyana hakan ne a yau Jumma'a, a wani taron manema labaru da aka kira a birnin Beijing na kasar Sin. Ya ce a fannin tsarin al'amuran duniya, kasar Sin na fatan ganin an kafa wata sabuwar huldar kasa da kasa, irin ta girmamawa juna, da nuna adalci da daidaito, da neman yin hadin gwiwa don cimma nasarori tare. Wannan buri da kasar Sin ta sanya, a hakika ba zai zamo hanyar ta da hankalin wani ba, illa ma dai hanya ce ta wanzar da zaman lafiya, da bukatar ci gaban dukkan kasashen duniya.
Saboda haka jami'in ya bukaci kasashen da batun da shafa da su lura da kyakkyawar rawa mai ma'ana da kasar Sin take takawa a harkokin da suka shafi gamayyar kasa da kasa.(Bello Wang)