Babban masanin kimiyya na WMO, Omar Baddour, ya fadawa 'yan jaridu a birnin Geneva cewa, wadannan shekarun 3 su ne mafiya zafi da aka samu a tarihi inda shekarar 2016 ta shiga cikin tarihi, sai shekarar 2017 take bi mata baya a matsayin mafi zafi ba tare da fuskantar sauyin yanayi na El Nino ba, wanda ka iya kara yawan dumamar yanayin duniya a duk shekara.
Baddour yace, shekarar 2017 itace shekara ta biyu mafi zafi tare da shekarar 2015. Shekarar da ta shiga tarihi itace 2016, saboda tasirin matsalar sauyin yanayi na El Nico. Yace idan aka dauke batun tasirin na sauyin yanayin na El Nino, shekarar 2017 itace shekara mafi zafi ba tare da samun sauyin yanayin na El Nino a shekarar ba.
"Babban labarin ba dumama yanayi ba ne, sai dai sauyin yanayi", inji Baddour.
Wata sanarwa da ya fitar, sakatare janar na WMO, Petteri Taalas, ya bayyana cewa, "sauyin yanayi na dogon zango shi yafi muhimmanci maimakon yin kididdigar shekara shekara, kuma wannan al'amarin yana cigaba da karuwa".
Ya kara da cewa, shekaru 17 daga cikin 18 mafiya zafi da aka taba samu a tarihi, sun faru ne a cikin wannan karni, kuma ma'aunin yanayin zafi na wadannan shekarun 3 da suka gabata sun kasance na daban ne. (Ahmad)