in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
GDP na kasar Sin ya karu da kaso 6.9 bisa dari a shekarar 2017
2018-01-19 10:42:13 cri

Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a jiya Alhamis sun nuna cewa, a shekarar 2017 da ta gabata, adadin GDPn kasar Sin ya kai yuan biliyan dubu 82 da 700, kwatankwacin dalar Amurka biliyan dubu 12, karuwar kaso 6.9 bisa dari akan na shekarar 2016. Shugaban hukumar kididdigar kasar Sin Ning Jizhe ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar ta Sin yana tafiya yadda ya kamata a bara, kana za a ci gaba da kokari domin kyautata ingancin karuwarsa.

Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a shekarar 2017 da ta gabata, adadin GDP na kasar Sin ya kai kudin Sin yuan biliyan dubu 82 da 700, kwatankwacin dalar Amurka biliyan dubu 12, adadin da ya karu da kaso 6.9 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2016, wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta cimma burin samun karuwar tattalin arziki a cikin shekaru bakwai da suka gabata, wato a baya bai kai kaso 6.9 bisa dari ba. Shugaban hukumar kididdigar kasar Sin Jing Jizhe yana ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana tafiya lami lafiya, kana kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya, yana mai cewa, "A baya kasar Sin ta samu karuwar tattalin arziki ne ta hanyar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje kawai, amma yanzu ana cimma wannan burin ne ta wannan hanyar da kuma hanyar shigo da kayayyaki daga waje. A shekarar bara, yawan kayayyakin da aka fitar zuwa ketare ya kai kaso 10.8 bisa dari, kana yawan kayayyakin da aka shigo da su daga waje ya kai kaso kusan 20 bisa dari. Ana iya cewa, ba ma kawai bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ta amfanawa al'ummun kasar ta Sin ba, har ma ta taimaka matuka wajen ci gaban tatatlin arzikin fadin duniya, wanda ya kusan kaso 30 bisa dari."

A shekarar da ta gabata, adadin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kudin Sin yuan biliyan dubu takwas, kwatankwacin dalar Amurka biliyan dubu daya da dari biyu, adadin da ya yi daidai da matsayi na 14 da ta kai a fadin duniya a shekarar 2016.

Game da karuwar tattalin arzikin da kasar ta samu, masanin tattalin arziki a bankin Zhongyuan wato ZYB Wang Jun ya bayyana cewa, hakan yana da nasaba da gyaran fuskar da ake gudanarwa kan aikin samar da kayayyaki a kasar Sin a cikin shekaru biyu da suka gabata, ya ce, "An samu babban sakamako a fannin rage kayayyakin da ba a bukata, lamarin da ya saukaka sabanin dake tsakanin masu samar da kayayyaki da masu bukatar kayayyaki, haka kuma farashin kayayyakin da ake bukata ya karu, ribar da kamfanonin kasar suke samu ta karu cikin sauri, kana adadin kudaden da jama'a ke kashewa ya karu, aikin samar da hidima a kasar ya kyautata, duk wadannan sun taimaka wajen karuwar tattalin arziki a kasar ta Sin."

Alkaluman sun nuna cewa, kasar Sin ta samu ci gaba a fannin kirkire-kirkire, shugaban hukumar Ning Jizhe ya bayyana cewa, "A shekarar bara, an samu wasu manyan sakamako a fannin kirkire-kirkire, misali jirgin saman fasanja samfurin C919, da layin dogo mai saurin tafiya, da wayar sadarwa ta zamani, da aikin bincike a karkashin teku da sauransu, kana an samu babban ci gaba wajen kera na'urar mutum mutumin inji da mota mai aiki da wutar lantarki, har karuwarsu ta kai kaso 50 bisa dari, ban da haka kuma, adadin kayayyakin da aka sayar ta yanar gizo ya karu da kaso 28 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2016, adadin ayyukan jigilar kayayyaki cikin sauri shi ma ya karu da kusan kaso 30 bisa dari."

Bisa karuwar tattalin arziki a kasar Sin, rayuwar Sinawa ta samu kyautatuwa sannu a hankali, kudin shiga da al'uumun kasar ke samu sun karu da kusan kaso 7.3 bisa dari, adadin da ya zarta adadin karuwar GDP na kasar. Kana adadin mazauna birane da garuruwa a fadin kasar wadanda suka samu guraben aikin yi a bara ya kai sama da miliyan 13, farashin kayayyaki bai yi wani gagarumin sauya ba. Kazalika adadin Sinawa wadanda suka tafi kasashen waje domin yawon bude ido a bara ya kai miliyan 129, adadin kudin da aka samu daga shirya fina-finai ya kai kudin Sin yuan biliyan 50, adadin Sinawa wadanda suka saba zuwa motsa jiki ya kai kaso 50 bisa dari, ko shakka babu aikin samar da hidima ya taka mihimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arziki a kasar Sin.

Shugaban hukumar kididdigar kasar Sin Ning Jizhe ya bayyana cewa, kasar Sin tana hanzarta gudanar da kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, kuma ana sa ran cewa, tattalin arzikin kasar ta Sin zai ci gaba da karuwa da inganta a shekarar 2018 da muke ciki kamar yadda ake fata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China