in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin a MDD ya yi kira da a daidaita matsalar Libya ta hanyar siyasa
2018-01-18 11:23:55 cri
Mukaddashin jakadan kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya Wu Haitao ya bayyana jiya Laraba cewa, ya kamata kasashe daban daban su himmatu wajen daidaita batun kasar Libya ta hanyar siyasa, a wani mataki na kirkiro yanayin shawarwari da ya dace tsakanin bangarori masu ruwa da tsaki kan batun Libya.

A yayin taron da kwamitin sulhun MDD ya shirya jiya dangane da batun Libya, Wu Haitao ya ce, jama'ar Libya ne ya kamata su yanke shawara kan makomar kasarsu, a don haka ya zama dole kasashe daban-daban su mutunta cikakken 'yancin kasar Libya.

Wu Haitao ya kuma jaddada cewa, ya kamata bangarori masu ruwa da tsaki na Libya su yi hakuri da juna tare da hawa teburin shawarwari don daidaita sabanin ra'ayin dake tsakaninsu, su kuma lalubo bakin zaren daidaita matsalar ta hanyar siyasa.

Har wa yau, Wu ya ce, kasar Sin na goyon-bayan duk wani matakin domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare kuma da daidaita matsalar Libya ta hanyar siyasa. Kazalika, Sin na nuna goyon-baya ga kokarin da bangarori daban-daban suke yi na yaki da ayyukan ta'addanci a Libya.

Wu Haitao ya ce, ya kamata MDD ta kasance a kan gaba wajen shiga tsakanin matsalar Libya. Sin na fatan kasashen dake makwabtaka da Libya, da kungiyar tarayyar Afirka da gamayyar kasashen Larabawa da kungiyar tarayyar Turai za su kara kaimin samar da goyon-baya ga Libya. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China