in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron karawa juna sani na kwararrun kasar Sin da kasashen Afrika a birnin Beijing
2018-01-18 10:36:47 cri


An bude taron karawa juna sani na kwararrun kasar Sin da kasashen Afrika a birnin Beijing, taken taron shine cigaban kasar Sin a sabon karni da sabbin damammaki ga hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika. A jawabinsa na bude taron Mataimakin shugaban hukumar kula da hadin gwiwar kasa da kasa CASS, Farfesa Cai Fang ya bayyana cewa, manufar shirya taron shine don karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika da kuma shirye shiryen gudanar da taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC wanda kasar Sin zata karbi bakuncinsa cikin wannan shekara.

Cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin ne ta dauki nauyin taron, kama cibiyar hadin gwiwar kasa da kasa da nazarin alamurran kasashen yammacin Asiya da Afrika ta kasar Sin ne ta shirya taron.

Kwararru da masana a fannoni da dama na kasar Sin da kasashen Afrika sun gabatar da kasidu a taron.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China