Kakakin rundunar Ayob Qassem ya bayyana cewa, sojojin ruwa dake aikin sintiri sun aiwatar da ayyukan ceto har sau biyu a jiyan inda gaba daya suka kubutar da 'yan cin rani 234.
Mr. Qassem ya ce, 'yan cin ranin sun samu matsala a kwale-kwalen da suke ciki ne, abin da ya sa suka tsaya a kan teku, kuma masu aikin sintiri sun cece su tare da kai su wani sansanin soja da ke birnin Tripoli.
Tun a wannan watan ne, aka samu karuwar ayyukan fasa kwabri a kasar Libya.
Tun a shekarar 2011, yanayin tsaro ya tabarbare a kasar ta Libya, kuma wasu 'yan cin rani suka mai da kasar wani zango a kan hanyarsu ta satar shiga wasu kasashen Turai ta tekun Meditareniya. (Lubabatu)