A wajen ganawar, mista Zhang Dejiang, ya ce majalissar wakilan jama'ar kasar Sin tana dora muhimmanci kan kokarin raya huldar dake tsakaninta da majalissun kasar Gabon wato na dattawa da na wakilai, sa'an nan tana son kara musayar ra'ayi tare da bangaren Gabon kan al'amuran kafa dokoki, da sa ido kan yadda ake bin dokokin, gami da aikin gudanar da mulki.
A nata bangaren, madam Milebou ta ce, bangaren Gabon na son karfafa hadin gwiwa tare da kasar ta Sin, don kara kyautata huldar dake tsakaninsu. (Bello Wang)