in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a son barin kowace kasar Afirka baya a hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka
2018-01-17 11:43:42 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a jiya Talata cewa, ba a son a bar kowace kasar Afirka a baya a hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka.

Ministan ya fadi haka ne a lokacin da ya gana da manema labarai tare da takwaransa na kasar Sao Tome and Principe bayan ganawarsu a Sao Tome, babban birnin kasar, inda wani dan jarida ya yi tambaya game da ra'ayinsa a kan yadda har yanzu wasu kasashen Afirka kalilan ke huldar diflomasiyya tare da bangaren Taiwan.

Mr.Wang Yi ya ce, a halin yanzu, Sin na gaggauta hadin gwiwa tare da kasashen Afirka daga dukkan fannoni, musamman bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da kuma shawarar raya ziri daya da hanya daya, don taimaka wa kasashen Afirka tabbatar da bunkasar tattalin arziki da rayuwar al'ummominsu. Duk da haka, akwai wasu kasashen Afirka kalilan da har yanzu ke huldar diplosiyya tare da yankin Taiwan, abin da kuma ya hana su kulla hulda da kasar Sin da sa hannu kan hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka kamar yadda ya kamata, kuma hakan bai dace da muradun kasashen da kuma al'ummarsu ba. Don haka, yana fatan ba za a bar kowace kasar Afirka a baya ba a hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen na Afirka.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China