Shen Ying ta bayyana a yayin taron manema labarai da majalisar gudanarwar kasar ta kira a jiya, cewar kamfanonin sadarwa mallakar gwamnati sun kara inganta harkokinsu na sadarwa tare kuma da rage kudin da ake biya, a yayin da kamfanonin sarrafa man fetur da na samar da wutar lantarki suka yi kokarin tsimin makamashi tare kuma da rage hayakin da suke fitarwa, matakin da ya kai su ga rage kudi kimanin yuan biliyan 200. Har wa yau, sun kuma taimaka ga saukaka fatara a kasar, inda suka zuba jarin da ya kai kimanin yuan biliyan 20. (Lubabatu)