in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in siyasar kasar Sin ya gana da shugaban majalisar dattijan Gabon
2018-01-17 09:23:24 cri

Babban jami'i kwamitin bada shawara kan harkokin siyasar kasar Sin Yu Zhengsheng, ya tattauna da shugaban majalisar dokokin kasar Gabon Lucie Milebou a jiya Talata.

Yu wanda shi ne shugaban kwamitin bada shawara kan al'amurran siyasar kasar Sin (CPPCC) ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Gabon su goyawa junansu baya game da batutuwan da suka shafi muradun kasashen da kuma muhimman batutuwan da za su karfafa ci gaban mu'amalar siyasa tsakanin kasashen biyu.

Ya ce babban taron jam'iyyar kwaminis karo na 19 da aka gudanar a watan Oktoban shekarar da ta gabata ya nuna matsayin kasar Sin na nuna goyon baya da kuma kyautata mu'amala tsakaninta da kasashe masu tasowa, wanda hakan zai samar da sabbin damammaki game da hadin gwiwar Sin da Gabon da kuma ci gaban nahiyar Afrika.

Kasar Sin za ta taimakawa Gabon wajen samun sabbin ci gaba kuma tana maraba da kasar Gabon don shiga taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC wanda kasar Sin za ta karbi bakuncins a cikin wannan shekara, in ji mista Yu.

Milebou ya ce kasar Gabon tana daukar dangantakar dake tsakaninta da Sin da muhimmanci, kana majalisar dattijan kasar ta Gabon za ta kara karfafa kyakkyawar alaka da CPPCC. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China