in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi shawarwari tare da ministan harkokin wajen kasar Sao Tome and Principe
2018-01-16 19:45:50 cri
A daren ranar 15 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Sao Tome and Principe Urbino Botelho.

A gun shawarwarin, Wang Yi ya bayyana cewa, ba zai manta da daddale hadaddiyar sanarwa ta sake kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Sao Tome and Principe tsakanin sa da Mr. Botelho, wanda suka yi shekara daya da ta gabata a nan birnin Beijing.

Ya ce a cikin shekara daya, an raya dangantaka tsakanin kasashen biyu cikin sauri a dukkan fannoni, an kuma kara yawan musaya tsakanin jama'ar kasashen biyu, da gudanar da ayyukan rukunin masana a fannonin samar da wutar lantarki, da yaki da cutar malaria, da bada jinya da kiwon lafiya da dai sauransu. Kaza lika bangarorin biyu sun kara yin hadin gwiwa a fannonin samar da ayyukan more rayuwa, da yawon shakatawa, da aikin noma da kamun kifi da sauransu.

An shaida cewa, kudurin sake kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasar Sao Tome and Principe da kasar Sin kuduri ne da ya dace, wanda ya yi daidai da yanayin zamani da bukatun jama'a, ya kuma kawo babbar moriya ga jama'ar kasashen biyu musamman ga jama'ar kasar Sao Tome and Principe.

Wang Yi ya jaddada cewa, Sin na daukar ra'ayi kan nuna daidaito ga kasashe manya da kanana, da nuna goyon baya ga kasar Sao Tome and Principe a hanyar ta ta samun bunkasuwa mai dacewa, kana tana fatan kara yin mu'amala tare da kasar Sao Tome and Principe, don tabbatar da moriyar kasashen biyu da ma kasashe masu tasowa gaba daya. Har ila yau kasar Sin tana maraba da kasar Sao Tome and Principe, ta yadda za ta zama sabuwar mamba a dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da zuwan wakilan kasar nan kasar Sin, don halartar taron koli na birnin Beijing.

A nasa bangare, Botelho ya bayyana cewa, sake kulla dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, kuduri ne mai dacewa wanda gwamnatin kasar Sao Tome and Principe ta tsaida, kuma kasarsa za ta tsaya tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya. Kana kasar Sao Tome and Principe ta nuna gamsuwa ga ci gaban da aka samu kan hadin gwiwar kasashen biyu a dukkan fannoni a cikin shekara daya, kana yana maraba da kamfanonin Sin wajen kara shiga aikin gina ayyukan more rayuwa, da raya aikin noma da kamun kifi da dai sauransu.

Ya ce kasar Sao Tome and Principe ta nuna goyon baya ga gudanar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da goyon bayan kasar Sin wajen gudanar da taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka a birnin Beijing. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China