in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta ce da alamun tattalin arzikin kasar zai inganta a wannan shekara
2018-01-16 08:47:48 cri

Mahukuntan Najeriya sun bayyaya tabbacin cewa, tattalin arzikin kasar zai inganta nesa ba kusa ba a shekarar 2018 da muke ciki, idan aka yi la'akari da alkaluman ci gaban da aka samu tun lokacin da kasar ta fita daga matsin tattalin arziki a rubu'i na biyu na shekarar da ta gabata.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ministan kasafin kudi da tsare-tsare na Najeriya Udoma Udo Udoma, ya ce ra'ayin gwamnatin Najeriya da na hukumomin dake auna karfin tattalin arzikin kasa na gida da na waje, game da bunkasar tattalin arzikin kasar cikin hanzari a wannan shekara ya zo daya.

Ministan ya kara da cewa, gwamnati ta himmatu wajen daukar matakan da suka dace na samar da damammaki na zuba jari a fannonin aikin gona, da kayayyakin gona da ake sarrafawa, da masana'antu da hakar ma'adinai, gine-gine da kuma ayyukan samar da hidima, duk da nufin bunkasa tattalin arzikin kasar.

A don haka ya yi kira ga sassa masu zaman kansu da dukkan masu ruwa da tsaki, da su shiga a dama da su, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China