in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Palestinu ya sake jaddada kin amincewa da shiga tsakanin Amurka cikin rikicin Palestinu da Isra'ila
2018-01-15 14:13:40 cri
Jiya Lahadi, a birnin Ramallah, shugaban al'ummar Palasdinawa Mahmoud Abbas ya sake jaddada cewa, Palestinu ba za ta yarda Amurka ta zama mai shiga tsakani a rikicin Palestinu da Isra'ila ba.

Yayin da yake gabatar da jawabi a wajen bikin bude taron gaggawa na kwamitin tsakiya na kungiyar PLO a birnin na Ramallah, Abbas ya ce, ba zai yarda Amurka ta nuna mulkin danniya ba. A cewarsa, za su yi la'akari da hanyoyi daban-daban da za su bi wajen daidaita rikicin bangarorin biyu, amma Amurka ba ta ciki.

Abbas ya kuma ce, Palestinu za ta ci gaba da tuntubar masu son shimfida zaman lafiya na Isra'ila, a wani kokari na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin bangarorin biyu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China