in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya musanta kalaman da ke cewa, wai yadda kasar Sin take tallafawa kasashen Afirka da kudade ya kara yawan basussukan da ake binsu
2018-01-15 11:34:18 cri

Bayan ganawar ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Angola Manuel Domingos Augusto, sun kuma gana da manema labarai, inda Mr.Wang Yi ya bayyana wasu ka'idoji uku da kasar Sin ke bi wajen tallafa wa kasashen Afirka da kudade, ya kuma musanta kalaman da ke cewa, wai yadda kasar Sin take tallafawa kasashen Afirka da kudade ya kara yawan basussukan da ake binsu.

A yayin taron manema labaran, wani dan jaridar ya tambayi ministan cewa, mene ne ra'ayin kasar Sin a kan furucin da wasu suka yi cewa, wai yadda kasar Sin take tallafawa kasashen Afirka da kudade ya kara yawan basussukan da ake binsu. A game da tambayar, Mr.Wang Yi ya ce, ai wanda ya yi wannan furuci yana da wata manufa ta fadin haka, kuma furucin sam ba shi da tushe. Ministan ya ce, a yayin da hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ke ci gaba da bunkasa cikin 'yan shekarun baya, a zahiri kasar Sin ta kara tallafa wa kasashen Afirka da kudade. Duk da haka, kasar Sin tana da wasu ka'idojin da take bi.

"Na farko, muna tallafa wa kasashen Afirka ne don biyan bukatunsu na raya kansu. Duk wata kasar da ke kan matakin bunkasa tattalin arziki da masana'antu na bukatar makudan kudade, kuma haka ma kasashen Afirka. Don haka, yadda kasar Sin take tallafawa kasashen Afirka da kudade gwargwadon karfinta bisa ga bukatar da suka bayyana, ya taimaka wa bunkasar tattalin arziki da rayuwar al'ummar kasashen, matakin kuma da ya samu amincewa da karbuwa daga kasashen."

Ka'ida ta biyu kuma ita ce, kasar Sin ba ta ko taba gindayawa ko wace kasa sharudan siyasa ba. Mr.Wang Yi ya ce, kamar yadda kasashen Afirka suka fuskanta, ita ma kasar Sin ta taba fuskantar zalunci da wasu kasashe suka yi mata a tarihi. Ya ce, "A sabili da haka, kasar Sin ba za ta bi kasashen yammaci ba ko ta fannin samar da gudummawa ko kuma wajen aiwatar da hadin gwiwa, balle ma a ce a tilasta mata. A maimakon haka, za ta rika mutunta kasashen Afirka tare da samar musu taimako."

Ka'ida ta uku ita ce samun moriyar juna. Hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka hadin gwiwa ce ta kasashe masu tasowa, kuma wani muhimmin bangare na hadin gwiwar kasashe masu tasowa shi ne zaman daidaito da kuma samun moriyar juna, abin da kuma zai kai ga samun dorewar hadin gwiwar da kuma bunkasuwar sassan biyu. Ya ce, "Don haka, ya zama dole kasar Sin ta tantance shirin hadin gwiwar da za a aiwatar ta fannin yiwuwar aiwatarwa da kasuwanci kafin ta fara samar da kudade, don tabbatar da cewa za a cimma muradun shirin ta fannin tattalin arziki da rayuwar al'umma."

Ministan ya jaddada cewa, wasu kasashen Afirka sun dade da fuskantar matsalar basussuka, an kuma gano bakin zaren warware matsalar, wato tabbatar da dauwamammen ci gaba da bunkasa tattalin arziki ta fannoni da dama. Kasar Sin tana kuma nuna cikakken goyon bayanta, tana kuma son ba da gudummawarta ta fannin inganta kwarewar kasashen Afirka wajen raya kansu, da tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da rayuwar al'ummar kasashen yadda ya kamata, ya ce, "Muna farin cikin ganin cewa, tattalin arzikin kasashen Afirka ya fara farfadowa daga bara, kuma kasashen Afirka sun fahimci muhimmancin tabbatar da dauwamammen ci gaban tattalin arziki. Tattalin arzikin kasashen Afirka na da makoma mai kyau."

Mr.Wang Yi ya kara da cewa, akwai wata karin magana a kasar Sin da ke cewa, ko takalma ya dace ko bai dace ba sai kafa ta sani, haka ma kasashen Afirka ne za su iya fada a game da hadin gwiwarsu da kasar Sin, ya ce, "Akwai kuma wani karin magana na daban da ke cewa, kowa na da adalci a zuci. Wane ne ya ke taimaka wa kasashen Afirka da gaske kuma wane ne aminin da kasashen Afirka za su iya amincewa da shi, lalle, al'ummar kasashen Afirka ne za su yanke wannan shawara." (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China