in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin dake gabashin Libya sun zargi Turkiya da daukar nauyin ayyukan ta'addanci a kasar
2018-01-15 10:03:46 cri

Mai magana da yawun sojojin Libya mai hedkwata a gabashin kasar Ahmad Al-Mismari ya zargi kasar Turkiya da daukar nauyin ta'addanci a kasar tun ma kafin sojoji su fara yaki da ayyukan ta'addanci a kasar sama da shekaru uku da suka gabata.

Mismari wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a birnin Benghazi dake gabashin kasar, ya kuma yi Allah wadai da matakin kasar na Turkiya, yana mai cewa, za su hukunta kasar Turkiya da ma kamfanoninta dake kasar. Ya kuma zargi Turkiya da hada baki da Sudan a fannin bayanan sirri, tun bayan da shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdowan ya ziyarci kasashen Sudan da Tunisiya.

Ya ce, har yanzu majalisar wakilan Libyan ba ta canja hukumar binciken da ta kafa game da jirgin ruwan da aka kama dauke da abubuwan fashewa da ya fito daga kasar Turkiya ba.

Ya ce, wasu abubuwan fashewa da kasar Girka ta kama a wani jirgin ruwan kasar Libya kwanakin baya, wata babbar barazana ce ba ga Libya kadai ba har ma ga daukacin shiyyar.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ce ma'aikatar harkokin wajen kasar Libya ta bukaci kasar Girka da ta yi mata bayani game da binciken da ta yi kan jirgin ruwan da ta kama.

A jiya ne kuma manzon MDD dake Libya Ghassan Salame ya yi alkawarin bayar da bayani game da jirgin ruwan da aka kama.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China