in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Angola ta nanata kudurinta na martaba manufar Sin daya tak a duniya
2018-01-15 09:19:42 cri

Ministan harkokin wajen kasar Angola Manuel Domingos Augusto ya nanata kudurin kasarsa na martaba manufar kasar Sun daya tak a duniya. Ministan wanda ya bayyana hakan yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Sin Wang Yi wanda ke ziyara a kasar, ya ce kasarsa tana kuma goyon bayan batutuwan da suka shafi cikakkun yankuna da muradun kasar Sin, ciki har da tekun kudancin kasar Sin.

Augusto ya ce, Angola tana martaba alakar dake tsakaninta da kasar Sin, alakar da ministan ya ce, ta mutunta juna da tattauna daidai wa daida ce. Ya kuma yi alkawarin daukar matakan da suka dace na zurfafa musaya da hadin gwiwa a fannonin da suka shafi siyasa, diflomasiya, tattalin arziki, cinikayya da kuma al'adu.

Ya ce, a shirye Angola take ta hada kai da kasar Sin don samun nasarar shirya taron kolin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) wanda kasar Sin za ta dauki bakuncinsa a wannan shekara.

A nasa jawabin, Wanga Yi, ya ce tun lokacin da Sin da Angola suka kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu shekaru 35 da suka gabata, kasashen biyu sun kasance muhimman kawaye, kana manyan abokan cinikayya.

Wang Yi ya kara da cewa, alakar kasashen biyu a fannoni da dama, ta kasance abin misali ga kyakkyawan zumuncin moriyar juna dake tsakanin Sin da Afirka. Don haka ya yi kira ga sassan biyu da su kara zage damtse wajen karfafa amincewa da juna a fannin siyasa da taimakawa wajen kare muradun juna.

Wang ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da hada kai da Angola, da kuma daukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa, taron kolin FOCAC da kasar Sin za ta dauki bakuncinsa ya kasance mai fa'ida ga hadin gwiwar sassan biyu.

Firaministan kasar ta Sin dai ya ziyarci kasashen Afirka ne a ziyararsa ta farko a sabuwar shekara, ziyarar da ta kai shi kasashen Rwanda da Angola. Daga bisani ne kuma ake sa ran zai ziyarci kasashen Gabon da Sao Tome and Principe.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China