in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kusa a jam'iyyar ANC ta Afrika ta kudu ta yiwa Trump raddi kan kalaman cin zarafin da ya furta
2018-01-13 13:05:48 cri
Wata babbar jami'a ta jam'iyyar ANC mai mulkin Afrika ta kudu a jiya Juma'a ta mayar da martani ga kalaman cin zarafi da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi, kan kasashe masu tasowa.

Shi dai Trump, ya yi amfani da kausasan kalamai na cin mutunci, inda ya bayyana kasashe masu tasowa a matsayin wulakantattu, mataimakiyar sakatare janar na jam'iyyar ta ANC Jessie Duarte, ta yi martanin ne a lokacin zantawa da manema labarai.

Shugaban na Amurka yana cigaba da fuskantar suka a cikin kasarsa da kasashen waje, bayan da aka rawaito shi yana danganta kasar Haiti da kasashen Afrika da cewa kaskantattu ne a lokacin da yake tattaunawa da 'yan majalisar dokokin kasar Amurkan kan batun dokar 'yan cin rani a fadar White House a ranar Alhamis din da ta gabata. Sai dai daga bisani shugaba Trump ya musanta kiran wata kasa a Afrika ko ma wata kasa a duniya da suna wulakantacciya, ya ce tabbas yayi amfani da kalamai masu kaushi, amma an yiwa kalaman nasa gurguwar fahimta.

Sai dai duk da musanta kalaman da mista Trump din ya yi, hakan bai kawar da damuwar da kasashe masu tasowa suka nuna game da kalaman nasa ba.

Duarte ta ce, duk da kasancewar kasashe masu tasowa suna fuskantar matsaloli, amma su ba wulakantattu bane, inda ta bayyana kalaman na Trump da cewa abin takaici ne.

Shima shugaban jami'yyar adawa ta Democratic Alliance (DA) Mmusi Maimane, ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, kalaman da Trump din yayi ya nuna a fili manufar da shugaban na Amurka ke da ita na kyamar kasashen Afrika da kuma fifita nuna wariyar launin fata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China