in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin ciniki tsakanin kasar Sin da kasashen da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa ya wuce kudin Sin yuan biliyan 7370
2018-01-12 15:20:02 cri

Wasu alkaluma da hukumar kwastan ta kasar Sin ta gabatar a ranar 12 ga wata sun nuna cewa, a shekarar 2017 da ta wuce, yawan kudin ciniki tsakanin kasar Sin da kasashen da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa, ya wuce kudin Sin yuan biliyan 7370, adadin da ya karu da kashi 17.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci a shekarar da ta gabace ta. Kuma wannan karuwa ta haura wadda kasar Sin ta samu ta fuskar yin ciniki da kasashen ketare da kashi 3.6 cikin dari, kana kuma, adadin ya kai kashi 26.5 cikin dari, bisa jimillar kudin da kasar Sin ta samu ta fuskar cinikayya da kasashen ketare. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China