in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya jaddada cewa, za a inganta yanayin siyasar CPC
2018-01-12 11:14:33 cri

Jiya Alhamis da safe, an shirya cikakken taron hukumar ladaftarwa da sanya ido ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na biyu a nan birnin Beijing, inda babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping ya jaddada cewa, a sabon zamanin da ake ciki yanzu, dole ne a gudanar da babban sha'anin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin karkashin jagorancin JKS, a saboda haka ya zama wajibi a kara inganta yanayin siyasar jam'iyyar.

Babban sakatare Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu kamata ya yi a kara inganta yanayin siyasa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta hanyar aiwatar da manufofin da aka tsara a yayin babban taron wakilan jam'iyyar karo na 19 daga duk fannoni karkashin jagorancin jam'iyyar, kuma, idan ana son cimma wannan buri, dole ne a kara mai da hankali kan yaki da cin hanci da rashawa, don haka za a kara karfafa karfin kirkire-kirkire da hadin kai na jam'iyyar, a karshe dai za a tabbatar da zaman al'umma mai matsakaicin karfi da gurguzu na zamani a nan kasar Sin yadda ya kamata. Xi ya bayyana cewa, "Yanayin siyasa na jam'iyyarmu yana da muhimmanci matuka ga babban sha'aninmu na tabbatar da zamantakewar al'umma mai matsakaicin karfi, da gurguzu na zamani a nan kasar Sin, a saboda haka ya zama wajibi a kara inganta yanayin siyasa na jam'iyyar, kana dole ne a gudanar da babban sha'anin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin karkashin jagarancin JKS."

Xi ya kara da cewa, tun bayan da aka shirya babban taron wakilan jam'iyyar JKS karo na 18, mun gano cewa, akwai matsalar yayin da muke kokarin kyautata yanayin siyasa na jam'iyyar, shi ya sa mun mai da hankali kan aikin, yanzu haka mun samu sakamako a bayyane, Xi yana cewa, "Mun samu sakamakon ne bayan matukar kokari da muka yi, shi ya sa kamata ya yi mu ci gaba da yin kokari tare, mu kuma kara himmantuwa kan wannan aiki."

Xi ya jaddada cewa, dole ne a nace ga manufar nan ta inganta yanayin siyasa na jam'iyyar cikin dogon lokaci, ya ce, "Za mu ci gaba da yin kokarin inganta yanayin siyasa na jam'iyyar karkashin jagorancin kwamitin tsakiya na jam'iyyar, wato hukumomin jam'iyyar su aiwatar da daukacin manufofin da kwamitin tsakiya na jam'iyyar ya tsara, kana a ko da yaushe jagororin jam'iyyar su gudanar da aikinsu karkashin jagorancin jam'iyyar JKS."

Xi ya ci gaba da cewa, ya fi muhimmanci a aiwatar da manufofin da kwamitin tsakiya na jam'iyyar ya tsara a fannin yaki da cin hanci da rashawa, kuma dole ne 'yan jam'iyyar su yi cudanya da sauran al'ummun kasar da ba 'yan jam'iyyar ba, da haka za su sa ido kan aikin 'yan jam'iyyar yadda ya kamata. "Ya kamata a gyara kuskure cikin lokaci, dole ne 'yan jam'iyya su yi cudanya da sauran al'ummun kasar da ba 'yan jam'iyyar ba ne, saboda abu mafi muhimmanci shi ne a mai da hankali kan babbar moriyar al'ummun kasar, wato kamata ya yi a yi kokarin warware matsalolin dake gaban su."

Xi ya yi nuni da cewa, idan ana son cimma burin nan na inganta yanayin siyasa na jam'iyyar JKS, to, dole ne a tsara manufofin da suka dace yayin da ake kokarin sa ido kan yanayin, kuma ya kamata a kyautata manufofin a ko da yaushe idan yanayin da ake ciki ya sauya, musamman ma a fannin yaki da cin hanci da rashawa, Xi yana mai cewa, "Ya zama wajibi a nace ga manufar inganta yanayin siyasa na jam'iyyar daga duk fannoni, kuma a ko da yaushe, wato ya kamata a kara daukar matakan da suka dace domin yaki da cin hanci da rashawa, ta yadda za a tsarkake yanayin siyasa na jam'iyyar. Kana idan ana son samu sakamako mai kyau, ya dace a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasarmu da sauran kasashen duniya."

Ban da haka, Xi ya kara da cewa, tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar karo na 18, hukumar ladaftarwa da sanya ido ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da sauran kananan hukumomin da abin ya shafa a fadin kasar sun samu sakamako mai faranta ran mutane, yana sa ran cewa, za su ci gaba da sanya kokari kan aikinsu a nan gaba。

Zaunannun mambobin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS Li Zhanshu da Wang Yang, da Wang Huning, da Han Zheng sun halarci taron, wanda ya samu jagorancin zaunannen mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kuma sakataren hukumar ladaftarwa da sanya ido ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Zhao Leji.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China