in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Filayen jiragen saman Xinjiang sun samu fasinjoji masu yawa a 2017
2018-01-12 11:11:21 cri

Filayen sauka da tashin jiragen sama 19 na jihar Xinjiang mai cin gashin kai ta kabilar Uygur dake arewa maso yammacin kasar Sin, sun samu fasinjoji sama da miliyan 30 a shekarar 2017 da ta gabata.

Alkaluma sun nuna yadda aka samu karuwar sufurin jiragen sama a jihar da kashi 14 bisa 100 a shekarar idan aka kwatanta da shekarar 2016, kamar yadda hukumar kula da sha'anin sufurin jiragen sama ta jihar ta tabbatar da hakan.

Haka zalika, filayen jiragen saman jihar sun yi dakon hajoji wadanda nauyinsu ya kai ton 188,000 a manyan jiragen dakon kaya da suka yi jigilar kayayyakin sau 359,000 a shekarar baran.

Samar da karin hanyoyin sufurin jiragen sama a jihar ya taimaka wajen samun karuwar fasinjojin a filayen jiragen saman yankin.

Ana samun bunkasuwar harkokin sufurin jiragen sama a Xinjiang. Adadin fasinjojin da filayen jiragen saman na Xinjiang suka yi jigilar su a shekarar 2010 sun kai miliyan 10 da miliyan 20 a shekarar 2014.

Jihar Xinjiang ta zuba jarin kimanin yuan biliyan 3.15, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 480 wajen aikin ginawa da fadada filayen jiragen saman jihar a shekarar da ta gabata, sama da kashi 230 bisa 100 idan aka kwatanta da shekarar 2016.

A halin yanzu akwai hanyoyin jiragen saman kimanin 49 a Xinjiang, wadanda suka gudanar da zirga-zirga kimanin 257 wadanda suke hade Urumqi, babban birnin jihar, da biranen kasar Sin 73 da biranen sauran kasashen duniya 24.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China