in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasuwar motoci masu aiki da lantarki a Sin ta samu bunkasuwa a 2017
2018-01-12 10:58:20 cri

Sabbin nau'ikan motoci masu aiki da lantaki na kasar Sin sun kara samun bunkasuwar ciniki a shekarar 2017, inda aka samu karuwar sayen motocin da kuma kera su da sama da kashi 50 bisa 100 a shekarar ta 2017, kamar yadda wata kididdiga da kungiyar masana'antun hada motoci ta kasar Sin ta tabbatar da hakan.

Kungiyar masana'antun kera motoci ta kasar Sin CAAM ta bayyana cewa, baki daya an sayar da sabbin motocin masu aiki da lantarki 777,000 a kasar Sin a shekarar da ta gabata, karin sama da kashi 53.3 bisa 100 idan an kwatanta da shekarar 2016.

An samu bunkasuwar wannan bangare ne sakamakon kokarin da kasar Sin ke yi na kara kaimi wajen amfani da makamashi mai tsabta a wani mataki na rage dumamar yanayi, inda gwamnatin kasar ke cire haraji ga kamfanonin dake samar da irin wadannan ababen hawan, da ba da rangwame ga masu sayen motocin, kana da ba da umarni ga ma'aikatun gwamnati da su dinga sayen sabbin motocin masu amfani da lantarki.

Bisa kididdigar shekarar 2017, kasar Sin ce ke kan gaba wajen kasuwar ababen hawa masu amfani da lantarki a duniya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China