in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gamayyar kasa da kasa sun yaba wa kasar Sin game da haramta cinikayyar hauren giwa
2018-01-11 13:31:26 cri

Tun daga ranar 1 ga watan Janairun bana, kasar Sin ta hana saye da sayar da hauren giwa a cikin gidanta baki daya, matakin da ya janyo yabo daga gamayyar kasa da kasa. Gwamnatin kasar Sin ta sanar da hana cinikin hauren giwa don neman dakile mugun aikin farautar namun daji daga tushe.

Asusun kiyaye namun daji (WWF) ya ba da sanarwa daga hedkwatarsa dake kasar Switzerland, wadda ke cewa, matakin da kasar Sin ta dauka zai yi tasiri matuka, ganin yadda manufar za ta taimakawa saukaka yanayin da ake ciki a kasashen Afirka, na satar farautar giwaye da kuma fataucin hauransu.

A cewar darektan asusun WWF mai kula da harkokin nahiyar Afirka Dokta Fred Kwame Kumah, kasar Sin tana taka rawar jagoranci a fannin kiyaye giwaye, wadanda suke rayuwa cikin daji ko kuma filin ciyayi.

A nasa bangaren, Tom Milliken, wani jami'i na kungiyar "Traffic International" da ke sa ido kan aikin fataucin halittu a duniya, ya ce matakin da kasar Sin ta dauka na hana cinikin hauren giwa ya nuna yadda kasar take kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta, ta fuskar kare namun daji, lamarin da zai karfafa niyyar gamayyar kasa da kasa ta dakile satar farautar namun daji.

Sa'an nan, a nashi bangare, babban darektan kungiyar kare giwaye ta kasar Botswana ko "Elephants Scents" Kenneth Sechele, ya ce, matakin da kasar Sin ta dauka na haramta cinikin hauren giwa, ya sa yawan hauren giwa da suke shiga cikin kasuwar kasar ya sauka da kashi 80%, don haka matakin zai haifar da sauye-sauye ga tarihin duniyarmu.

Ban da haka kuma, wasu masana da jami'ai na ganin cewa, matakin da kasar Sin ta dauka a wannan karo, zai zama wani abin misalin da za a koya a kokarin dakile satar farautar namun daji.

Wani masanin ilimin kare muhalli na kasar Rwanda, Greg Bakunzi, ya ce, wannan matakin da kasar Sin ta dauka ya mai da kasar abin koyi a duniya a fannin kare namun daji. Bisa wannan mataki ne, za a samu damar rufe sauran manyan kasuwannin sayar da hauren giwa a duniya, wadanda suke kasashen Japan, da Thailand, da Viet Nam, da dai sauransu.

A nasa bangaren, Kaddu Sebunya, shugaban asusun kare namun daji na Afirka (AWF), ya ce kasashen dake nahiya Afirka su ma kamata ya yi su koyi misali daga kasar Sin, su dauki takamaiman matakai a fannin kafa dokoki, don sauke nauyin dake bisa wuyansu na kare giwayen da suke cikin kasashen su.

A nashi bangare kuma, mamban kungiyar kare namun daji ta kasar Sri Lanka Vidya Abhayagunawaralena, ya ce yana fatan ganin kasar Sri Lanka ta koyi misalin kasar Sin a fannin daukar matakai masu karfi wajen kare giwaye, gami da sauran namun daji iri daban daban.

Haka zalika, wakilin asusun WWF a kasar Tanzania, Amani Ngusaru, ya yaba wa kasar Sin kan yadda ta cika alkawarin da ta dauka na haramta cinikin hauren giwa, da dakile satar farautar namun daji, inda ya yi kira ga sauran kasashen da ba su haramta cinikin hauren giwa ba tukuna, da su koyi misalin kasar Sin, don a dakatar da aikin saye da sayar da hauren giwa a duniya baki daya.

Ban da haka, jami'ai da masana na kasashe daban daban, suna sa ran ganin matakin haramta cinikin hauren giwa da kasar Sin ta dauka zai haifar da sauye-sauye ga duniyarmu.

A cewar Vidya Abhayagunawardena, mamban kungiyar kare namun daji ta kasar Sri Lanka, yadda kasar Sin ta haramta aikin fataucin hauren giwa zai tsoratar da mutanen da suke gudanar da wannan mummunar aiki a wurare daban daban na duniya.

Yayin da a nashi bangare, ministan muhalli da yawon shakatawa na kasar Botswana, Tshekedi Khama, ya ce matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka a wannan karo zai haifar da dama ga yunkurin kare giwaye a nahiyar Afirka.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China