in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suke mutuwa ko su bace a tekun Mediterranean ya yi matukar karuwa
2018-01-11 13:29:58 cri
Hukumar kula da bakin haure ta duniya mai cibiya a birnin Geneva ta bayyana a jiya Laraba cewa, a kwanaki 9 na farkon watan Janairun bana, mutane kusan 200 ne suka mutu ko suka bace yayin da suka ratsa tekun Mediterranean ba bisa ka’ida ba, adadin da ya yi matukar karuwa bisa na watan da ya gabata. Rahotanni sun bayyana cewa, yawancin mutanen sun tashi ne daga kasar Libya a yunkurinsu na isa kasar Italiya. Wani hadari ya auku a ranar 9 ga wannan wata, kuma bayan faruwarsa, masu aikin ceto sun ceci mutane 279 a tekun dake dab da kasar Libya. Bisa labarin da mutanen da aka ceto suka bayyana, an ce, akwai mutane kimanin dari daya da suka bace a sakamakon hadarin. Bisa kididdigar da hukumar kula da bakin haure ta duniya ta yi, an ce, ‘yan gudun hijira ko bakin haure kimanin dubu 170 sun isa nahiyar Turai ta hanyar ratsa tekun Mediterranean a shekarar 2017, adadin da ya ragu da kashi 50 cikin dari bisa na shekarar 2016. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China