in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMB: An samu raguwar fashin teku da garkuwa da mutane
2018-01-11 10:13:44 cri

Wani rahoto da hukumar kasa da kasa mai kula da harkokin cinikayya da sufurin jiragen ruwa ko IMB a takaice ta fitar, ya ce yawan laifuka da ake aikatawa masu nasaba da fashin teku ko fashi da makami a ruwa ya ragu a shekarar 2017.

A shekarar da ta gabata, adadin laifuka masu alaka da hakan da aka samu ba su haura 180 ba, adadin da shi ne mafi karanci cikin 'yan shekarun nan, tun bayan shekarar 1995, lokacin da aka samu nau'in wadannan laifuka 188.

Rahoton na IMB ya kara da cewa, a baran, an samu aukuwar fashin teku 136, da yunkurin garkuwa da mutane 22, an kuma kaiwa wasu jiragen ruwa 16 farmaki da bindiga, yayin da kuma aka yi garkuwa da wasu jiragen 6.

Har ila yau rahoton ya ce a baran, an samu 'yan matsaloli kusan 36 a gabar tekun Guinea, ko da yake ba wani jirgi da aka yi garkuwa da shi, sai kuma wasu laifuka masu nasaba da sace mutane har karo 10, wadanda suka rutsa da ma'akatan jiragen ruwa 65 a sassan tekun Najeriya. Bisa jimilla an kaiwa jiragen ruwa 16 hari da bindiga a sassan tekunan duniya daban daban, ciki hadda na gabar tekun Guinea.

Duk dai da raguwar wadannan laifuka, IMB ta yi gargadin masu sufuri ta jiragen ruwa da kada su yi sakaci da tsaro, yayin da suke ratsa tekun Arabia da tekun Aden.

Da yake karin haske game da hakan, Daraktan hukumar ta IMB Pottengal Mukundan, ya ce gabar tekun Guinea, da ruwayen da suka ratsa tarayyar Najeriya na ci gaba da zama masu hadari ga masu safara ta ruwa, duk da cewa mahukuntan Najeriya na daukar matakan dakile wannan matsala.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China