in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana kara mai da hankali kan ingancin kayayyaki
2018-01-10 10:24:26 cri

Jiya Talata an kira taron aikin sa ido kan ingancin kayayyakin kasar Sin na shekarar 2018 a nan birnin Beijing, inda aka sanar da cewa, a cikin shekaru hudu da suka gabata, adadin kayayyakin kasar wadanda suka kai ma'aunin da aka tsara ya kai kaso 90 bisa dari, kana an bayyana cewa, nan gaba kasar za ta ci gaba da mai da hankali kan ingancin kayayyakin da ake samarwa.

A cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta samu babban sakamako wajen yin gyaran fuska kan tsarin tattalin arziki, da bude kofa ga kasashen waje, kana ta ciyar da babban sha'anin zamanintar da tsarin gurguzu a kasar gaba yadda ya kamata. Yayin taron aikin sa ido kan ingancin kayayyakin da aka shirya jiya, shugaban babbar hukumar kula da aikin sa ido kan ingancin kayayyaki ta kasar Sin Zhi Shuping ya bayyana cewa, a cikin wadannan shekaru biyar da suka gabata, matsayin ingancin kayayyakin kasar na dagawa sannu a hankali, haka kuma ana kara mai da hankali kan ingancin kayayyakin da ake samarwa a fadin kasar, ko shakka babu aikin sa ido kan ingancin kayayyaki na kasar Sin ya samu ci gaba bisa babban mataki, yana mai cewa, "Tun daga shekarar 2014, adadin kayayyakin kasar wadanda suka kai ma'aunin da aka tsara ya kai kaso 90 bisa dari, wasu kuwa sun zarta kaso 95 bisa dari, misali motoci da na'urorin injiniya na musamman, da magungunan sha da sauransu, ban da haka kuma ingancin kayayyakin da ake sayarwa ta yanar gizo shi ma ya kyautata a kai a kai. Har ila yau al'umma na nuna gamsuwa game da hakan."

A fannin tsaron kasa, hukumar kwastan ta kasar ta kafa tsarin bincike kan kayayyakin da ake shigowa da su daga ketare, domin magance shigo da halittu masu iya haifar da barna ga halittun kasar, musamman ma kan abinci. Game da annobar da ke aukuwa a fadin duniya kuwa, kasar Sin ita ma ta tura tawagar aiki zuwa kasashen waje domin shawo kan yaduwarta, matakin da ya kiyaye tsaron kasar, Zhi Shuping ya ce, "Mun yi kokari matuka domin yaki da annobar da ta yadu a fadin duniya a cikin shekaru biyar da suka gabata. Misali annobar Ebola, da ciwon shawara, da kwayar cuta ta Zika da sauransu. Game da ciwon shawara da ya yadu a kasar Angola kuwa, mun tura tawagar likita karo na farko zuwa kasar domin samar da allurar rigakafi ga Sinawa dake zaune a kasar, inda aka yi nasarar shawo kan yaduwar annobar cikin sauri."

Zhi Shuping ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu kasar Sin tana kara mai da hankali kan hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen waje a fannin sa ido kan ingancin kayayyaki, musamman ma yayin da ake kokarin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, ya ce, "Ana aiwatar da manufofin da kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya suka tsara cikin hadin gwiwa, ciki hadda aikin tsara ma'aunin ingancin kayayyaki, da aikin kididdiga kan nauyin kayayyaki, da samun amincewar ingancin kayayyaki, da aikin sa ido kan ingancin kayayyaki yadda ya kamata, har ma an kai ga gudanar da shawarwari tsakanin ministocin kasashen har sau 200, tare kuma da daidaita matsalolin da suka shafi amincewar shigar da kayayyakin da yawansu ya kai kusan 69 a cikin wadannan kasashen."

A shekarar 2017 da ta gabata, babbar hukumar kula da aikin sa ido kan ingancin kayayyakin kasar Sin, ta mayar da kyautatuwar ingancin kayayyaki a matsayi na koli yayin da take gudanar da aiki, daraktan ofishin babbar hukumar Lin Wei ya bayyana cewa, a cikin shekaru uku masu zuwa, kasar Sin za ta sanya kokari matuka domin kara kyautata ingancin kayayyaki a fadin kasar, ya ce, "Babbar hukumar kula da aikin sa ido kan ingancin kayayyakin kasar Sin, ta mayar da shekarar 2018 a matsayin shekarar kyautata ingancin kayayyaki. A saboda haka za ta yi kokari tare da sauran hukumomin da abin ya shafa, domin tabbatar da ingancin kayayyaki, ta yadda za a biya bukatun rayuwar al'ummun kasar yadda ya kamata."

Shugaban babbar hukumar kula da aikin sa ido kan ingancin kayayyaki ta kasar Sin Zhi Shuping ya fayyace cewa, bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, nan da shekarar 2035, kasar Sin za ta cimma burin kaiwa sahun gaba a fadin duniya a fannin ingancin kayayyaki.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China