in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi nasarar harba wasu taurarin dan Adam guda biyu
2018-01-09 13:37:23 cri

Da misalin karfe 11 da minti 24 na safiyar yau Talata ne, a cibiyar harba taurarin dan Adam dake birnin Taiyuan na kasar Sin, kasar Sin ta yi nasarar harba wasu taurarin dan Adam na zamani guda biyu, samfurin SuperView-1 mai lamba 3, da SuperView-1 mai lamba 4. Dukkan taurarin dan Adam sun shiga falaki kamar yadda aka tsara. Wannan shi ne karon farko da kasar Sin ta yi nasarar harba taurarin dan Adam zuwa sararin samaniya a cikin sabuwar shekara ta 2018.

Rahotanni na cewa, taurarin dan Adam din za su samar da muhimman bayanai da hidimomi ga masu sayayya a duk fadin duniya, a fannonin da suka shafi albarkatu, da safiyo, da taswira, da sa ido kan muhalli, da harkokin kudi da inshora da ma batun Intanet.

Cibiyar nazarin fasahohin sararin samaniya dake karkashin babban kamfanin kula da kimiyya da fasahar sararin samaniya na kasar Sin, tare da hadin gwiwar cibiyar nazarin fasahohin sararin samaniya dake birnin Shanghai ne suka kirkiro wadannan taurarin dan Adam guda biyu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China