in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayar da lambobin yabo a fannin kimiyya da fasaha ta shekarar 2017 a kasar Sin
2018-01-09 13:34:11 cri

An bayar da lambobin yabo a fannin kimiyya da fasaha ta shekarar 2017 a kasar Sin jiya Litinin. An ce, gaba daya aka bada lambobin yabo ga ayyukan binciken kimiyya da fasaha guda 271, da kuma masana masu ilmin kimiyya da fasaha guda 9, ciki har da masana biyu da suka samu lambobin yabo da suka fi daraja a wannan fanni, da ayyukan binciken kimiyya na halitta guda 35, da ayyukan kirkire-kirkire guda 66, da ayyuka guda 170 a fannin ci gaban kimiyya da fasaha, baya ga masana baki 7 da suka samu lambobin yabo na hadin gwiwa tare da Sin a wannan fanni.

Bisa wadannan ayyukan da suka samu lambobin yabon, muna iya ganin cewa, masana masu ilmin kimiyya na kasar Sin na samu babban ci gaba a wasu fannonin da ba a taba samun ci gaban su a baya ba. Lamarin da ya alamta cewa, kasar Sin na jagorantar ci gaban kimiyya da fasaha a duniya.

A lokacin bazara na shekarar 2013, wasu mazauna yankin delta na kogin Yangtse dake gabashin kasar Sin sun kamu da annobar murar tsuntsaye nau'in H7N9, lamarin da ya jawo hankalin kasashen duniya sosai. Domin shawo kan wannan sabuwar annobar, asibiti na farko a karkashin jagorancin kwalejin ilmin likitanci ta Jami'ar Zhejiang ta kafa wata kungiyar musamman ba tare da bata lokaci ba. Bisa kokarin da Li Lanjuan, kwararriyar Cibiyar Nazarin Ayyukan Injiniya ta kasar Sin da abokan aikinta suka yi tare, kungiyar ta samu babban ci gaba a fannonin gano sabbin kwayoyin cutar, da tabbatar da ababen yaduwar cutar, da tabbatar da tsarin kamuwa da cutar, da ba da jinya, da kirkirar sabuwar allurar rigakafin cutar da dai sauransu. Hakan ya sa wannan aikin ya samu lambar yabo ta koli a fannin samun babban ci gaban binciken kimiyya na shekarar 2017 ta kasar Sin.

Madam Li Lanjuan wadda ta jagoranci aikin ta bayyana cewa, bisa sakamakon aikin, an shawo kan yaduwar annobar murar tsuntsaye nau'in H7N9 a tsakanin mutane yadda ya kamata. Tana mai cewa,

"Da farko, mun tabbatar da cewa, kwayoyin cutar murar tsuntsaye sun samu sauyi, har ma ya sa mutane ke iya kamuwa da cutar. Sa'an nan mun tabbatar da cewa, bayan da aka kamu da cutar, jikin mutane ya fi samun saurin lalacewa, har ma hakan na haddasa mutuwar mutane. Ban da wannan, bayan da muka gano cewa, kwayoyin cutar da muka samu a jikin mutum sun yi kusan daidai da na tsuntsaye masu rai, mun tabbatar da cewa, mutane suna kamu da cutar ne bayan da suka taba tsuntsaye masu rai. A cikin wata guda kacal, mun sanar da wadannan labaru uku ga duk duniya. Lallai mun tinkari wannan annoba yadda ya kamata."

Bayan da suka yi bincike sosai, kungiyar dake karkashin shugabantar Madam Li Lanjuan ta sanar wa duniya cikin lokaci kan tsarin kwayar dabi'ar halitta ta murar tsuntsaye nau'in H7N9. Daga baya, a karon farko ta nuna alamun cutar, da kirkirar jerin sabbin fasahohi wajen rage yiyuwar mutuwar wadanda ke kamuwa da ita. Hakan ya sa aka samu wata sabuwar fasahar warkar da masu kamuwa da cututtukan dake yaduwa masu tsanani.

A cikin ayyukan binciken kimiyya da fasaha da suka samu lambobin yabo na bana, akwai wasu da ke kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a. kamar yadda aka sani, matsalar gurbata muhalli ta riga ta zama batun da ya fi jawo hankalin Sinawa a 'yan shekarun baya. Bisa sakamakon binciken da aka samu, an ce, kona kwal wani muhimmin dalili ne da ke haddasa bullowar hazo mai tsanani. Domin warware matsalar, furofesa Gao Xiang, shugaban kwalejin ilmin makamashi da injiniya ta Jami'ar Zhejiang ya jagoranci kungiyarsa wajen nazarin muhimmiyar fasahar rage yawan hayakin da na'urorin kona kwal suke fitarwa, wanda ya samu lambar yabo ta matsayin farko a fannin kirkire-kirkire ta wannan karo.

Furofesa Gao Xiang ya bayyana cewa, bayan da suka yi nazari har na tsawon shekaru fiye da 10, sun kirkira tsarin fitar da hayaki mafi kankanta, ko da yake a kan yi amfani da makamashi masu gurbata muhalli iri daban daban a sa'i daya. Gao Xiang ya ce, yanzu ana amfani da fasahar da suka samu a cikin na'urori fiye da 300 na kona kwal, wajen samar da wutar lantarki, ta yadda hakan ya taimaka sosai ga tsarin rage yawan hayakin da masana'antun samar da wutar lantarki ta hanyar kona kwal ke aiwatarwa. Ya kara da cewa,

"Bisa fasahohinmu, an rage yawan iskar sinadarin sulfur dioxide da kashi 83 cikin 100, da sinadarin nitrogen oxide da kashi 50 cikin 100, da kananan abubuwan da ke cikin iska da kashi 67 cikin 100. Don haka bayan da aka yi amfani da fasahohin, ba za a ci gaba da daukar masana'antun samar da wutar lantarki bisa karfin kwal matsayin masu fitar da iskar gas mai gurbata muhallin halittu ba."

Bugu da kari, Furofesa Gao Xiang ya furta cewa, yayin da aikin ke kokarin rage yawan hayakin da aka fitar, ya samu babban ci gaba a fannin sa kaimi ga bunkasar kimiyya da fasaha, kafa dandalin kirkire-kirkire, horar da kwararru. Abin da ya zamo mai amfani ga zamatakewar al'umma daga fannoni daban daban. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China