A yammacin Litinin din nan shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron a saukin bakin gwamnati na Diaoyutai dake nan birnin Beijing.
Shugaba Macron dai yana ziyarar aiki ne a nan kasar Sin daga yau Litinin zuwa ranar Laraba. Ya iso birnin Beijing ne yau da rana, bayan ziyarar tsawon rabin yini da ya kai birnin Xi'an dake arewa maso yammacin kasar Sin.(Ibrahim)